Tinubu Ya Sa Rana, Zai Ziyarci Binuwai bayan Kisan kusan Mutum 200
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce zai sauya jadawalin aikinsa domin kai ziyara ta musamman a jihar Binuwai a ranar Laraba
- Tinubu ya bayyana shirin kai ziyarar a yau, bayan ya sha suka daga yan adawa kan jinkirin ganewa idanunsa halin da ake ciki a jihar
- Shugaban ya shawarci mutanen jihar su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu, tare da zama al’umma daya don wanzuwar zaman lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zai soke wasu daga cikin ayyukansa domin kai ziyara ta musamman ga al’ummar jihar Binuwai a ranar Laraba.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake kaddamar da aikin samar da ruwan sha a babban birnin tarayya, Abuja.

Asali: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa shugaban kasar ya bayyana alhininsa kan mutanen da suka rasa rayukansu da kuma wadanda hare-haren suka rutsa da su a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya shawarci mutanen Binuwai
Solacebase ta ruwaito cewa Shugaban ya bukaci al’ummar jihar da su kar su dauki bambancin ra’ayoyinsu, fushi da bacin rai a matsayin abin da zai kawo masu sabani.
Ya ce kamata yayi duk da bambancin, su rike juna da amana a matsayin al'umma guda dake bukatar kwanciyar hankali da ci gaba.
Ya ce:
"Zan daidaita tsarin aikina na wannan makon, domin in kai ziyara ga mutanen Binuwai a ranar Laraba."
Kalamansa na zuwa ne bayan ya bayar da umarni ga jami'an tsaro da su gaggauta daukar matakan da za su dakatar da kashe jama'a da ake yi babu kakkautawa.
Binuwai: ‘Yan adawa sun caccaki Tinubu
Masu adawa da gwamnatin Tinubu, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Peter Obi, sun soki shugaban kasar bisa jinkirin kai ziyarar ta’aziyya Binuwai.
Jihar ta dade tana fuskantar hare-hare daga wasu da ake zargin makiyaya ne, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da lalata gidaje da gonaki.

Asali: Facebook
Hare-haren dai sun jima suna faruwa a jihar, wasu na danganta su da rikicin kabilanci da kuma takaddamar mallakar filaye tsakanin manoma da makiyaya.
A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, an samu hare-hare marasa yankewa a jihar, inda aka tabbatar da mutuwar sama da mutum 160 sakamakon hare-haren da ake zargin makiyaya ne suka kai.
Sarkin Musulmi ya magantu kan kisan Binuwai
A baya, kun samu labarin cewa ama’atu Nasril Islam, karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na Sakkwato, ta yi takaicin kisan mazauna jihar Binuwai.
JNI ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, inda ta bayyana cewa yin shiru kan wannan mummunan lamarin ba zai amfani zaman lafiyar kasa ba, sai dai kara jefa jama'a a rikici.
Kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su farka daga barci, su dauki matakin gaggawa domin kare rayukan 'yan kasa, tare da cafke wadanda ke da hannu a cikin wannan danyen aiki.
Asali: Legit.ng