Biyafara: Karairayin Ojukwu ne sanadiyar barkewan yakin basasa - Yakubu Gowon

Biyafara: Karairayin Ojukwu ne sanadiyar barkewan yakin basasa - Yakubu Gowon

- Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon (Murabus) ne ya fadi hakan

- Ya ce sun tafi Aburi na Kasar Ghana a inda su ka yi yarjejeniyar hadin kan Najeriya

- Shi kuwa Ojukwu sai ya bijirewa wannan yarjejeniyar, in ji Gowon

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya na mulkin Soja, Janaral Yakubu Gowon (Murabus), ya bayyana yadda Karairayin Odumegu Ojukwu, sabanin yarjejeniyar Aburi, ya sabbaba yakin basasa tsakanin 1967 zuwa 1970.

Gowon ya yi wannan bayani ne a yayin wani shiri a gidan talabijin din AIT. Ya ce sun tafi Aburi da ke Kasar Ghana ne don samun warware matsalolin da su ka addabi siyasar Kasar.

Karerakin Ojukwu ne sanadiyar yakin basasar Najeriya - Yakubu Gowon
Karerakin Ojukwu ne sanadiyar yakin basasar Najeriya - Yakubu Gowon

Ya ce an amincewa dukkan jawabi da matsayar da Ojukwu ya gabatar wanda dukkanin su su na nuni ga zaman lafiya ne da hadin kan Kasar. An kuma yi yarjejeniyar Gowon me zai fara gabatarwa 'yan Najeriya jawabi idan a ka dawo gida.

KU KARANTA: Kasar Saudiyya za ta sassauta tsauraran dokokin ta

Shi kuwa Ojukwu sai ya bijirewa yarjejeniyar ya fara gabatar da jawabi a gidan rediyo kuma jawabin na sa ya sabawa dukkan yarjejeniyar da aka yi ne. Gowon ya ce watakila Ojukwu ya yi hakan ne ganin yadda a ke kashe 'yan Kudu a Arewa.

Kisan 'yan kudun, wanda kwata kwata ba da sanin Hukuma ba ne, shi ya sa Ojukwu ya yi tunanin raba Kasar kadai shi ne mafita. Alhali ita gwamnati ta na bayan hadin kan Kasar ne.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164