An Gargadi 'Yan Siyasa kan Harin da 'Yan APC Suka kai wa Ganduje a Gombe

An Gargadi 'Yan Siyasa kan Harin da 'Yan APC Suka kai wa Ganduje a Gombe

  • Hadimin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Oliver Okpala, ya ce harin da aka kai wa Abdullahi Ganduje a taron APC na Arewa maso Gabas a Gombe ba abin yarda da shi ba ne
  • Okpala ya bayyana lamarin a matsayin rashin tarbiyya da rashin kishin kasa, yana mai gargadin mambobin jam’iyya da su guji siyasar tarzoma
  • Ya ce dangantakar Ganduje Bola Tinubu da Kashim Shettima tana da ƙarfi, kuma bai kamata wasu marasa biyayya su kawo rikici a kan batun tikitin 2027 ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hadimin shugaban APC, Cif Oliver Okpala ya bayyana harin da wasu 'yan jam’iyyar suka kai wa Abdullahi Ganduje a Gombe a matsayin abin Allah-wadai da rashin ladabi.

Okpala ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce tarzomar da ta faru a taron shiyyar Arewa maso Gabas na APC wata alama ce ta siyasar rashin natsuwa.

Ganduje ya yi martani kan harin da aka kai masa a Gombe
Hadimin Ganduje ya yi Allah wadai da harin da aka kai masa a Gombe. Hoto: Hassan Muhammad|Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Okpala ya ce harin da aka kai wa Dr Abdullahi Umar Ganduje lamari ne da ba shi da amfani ga demokuradiyyar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce irin wannan rikici ne ya janyo rugujewar jamhuriya ta farko a Najeriya, saboda haka ya zama dole a yi hattara kada irin wannan kuskure ya sake faruwa.

Alakar Ganduje da Tinubu da Shettima

Okpala ya jaddada cewa Ganduje mutum ne mai son zaman lafiya, kuma dangantakarsa da shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ba ta da wata matsala.

Ya ce duk da kokarin Ganduje na bayyana cewa tikitin shugaban kasa da mataimaki ɗaya ne bisa kundin tsarin mulki, wasu daga cikin mahalarta taron sun ƙi yarda da hakan.

Vanguard ta wallafa cewa Okpala ya ce:

“A fili Ganduje ya ce: ‘Arewa maso Gabas ce ta samar da mataimakin shugaban kasa, kuma jam’iyyar APC na alfahari da wannan yanki,’”

Batun kai wa Ganduje hari a Gombe

Okpala ya ce yayin da Ganduje ke kokarin shiga motarsa domin barin wajen taron, wasu mutane suka taso masa domin kai masa hari, amma sai jami’an tsaro suka yi gaggawar dakile lamarin.

Ya ce wannan harin ba wai a kan Ganduje kadai ba ne, har da gaba ɗayan shugabancin APC na ƙasa wanda ya wakilta.

Hadimin shugaban ya ce:

“A ce har a gaban gwamnoni daga yankin, wasu marasa kunya za su ɗauki wannan mataki, lamarin ya nuna rashin mutunci da rashin sanin darajar shugabanci,”
Hadimin Ganduje ya yi wa 'yan siyasa nasiha
Hadimin Ganduje ya bukaci a rika girmama shugabanni. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Kira ga shugabannin siyasa da magoya bayansu

Okpala ya yi kira ga shugabannin siyasa su gargadi magoya bayansu da su guji tashin hankali, yana mai cewa siyasa magana ce ta tattaunawa ba faɗa ba.

A cewar shi:

“Wannan abin da ya faru a Gombe ba zai ƙara wa jam’iyya ɗaukaka ba, sai dai ya kawo ɓarna da rarrabuwar kai."

Legit ta tattauna da Anas Salihu

Wani matashi dan APC a jihar Borno, Anas Salihu ya zantawa Legit cewa ko da ba hakan cikin tsarin mulki, ya kamata a Kashim Shettima ya yi takara a 2027.

Malam Anas ya ce:

"Shi ne babban wakilin Arewa maso Gabas a APC a yanzu. Idan ba a tafi da shi ba, mutanen yankin za su ji kamar jam'iyyar ba ta yi da su."

APC ta yi magana kan takarar Shettima a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi magana a kan rikicin da aka samu kan takarar Sanata Kashim Shettima a Gombe.

Hadimin shugaba Bola Tinubu, Daniel Bwala ya ce ba shi da wata masaniya kan cewa za a hana Shettima takara da Tinubu.

Shugaban APC a Kudu maso Gabas ya ce babu wata matsaya da jam'iyyar ta dauka domin hana Shettima zama mataimakin shugaban kasa a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng