Insha Allahu ba za'a taba wani yakin Basasa a Najeriya ba, Shugaba Buhari

Insha Allahu ba za'a taba wani yakin Basasa a Najeriya ba, Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tawagar shugabannin darkiar Tijjaniya

- Sun ziyarcesa domin gabatar masa da sabon Khalifan Sheikh Ibrahim Niass

- Daga cikin tawagar akwai babban malami, Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi waiwaye kan yakin basasan da aka kwashe watanni 30 ana yi a Najeriya kuma ya yi addu'a kada Allah ya maimaitawa Najeriya irin wannan yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake mai taken "Shugaba Buhari ya aika ta'ziyya ga shahidan yakin basasan Najeriya."

Najeriya, karkashin Janar Yakubu Gowon ta shiga yaki da Biyafara da suka balle karkashin jagorancin Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Junairun 1970.

Shehu ya ce Buhari ya yi waiwayen ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban mazhabar Tijjaniyya, Sheikh Muhammadul Mahy Niass.

DUBA NAN: Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai

Insha Allahu ba za'a taba wani yakin Basasa a Najeriya ba, Shugaba Buhari
Insha Allahu ba za'a taba wani yakin Basasa a Najeriya ba, Shugaba Buhari Credit: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ba ni ya taya ba, Ministan Buhari ya nisanta kansa daga Baturen zaben da aka jefa kurkuku kan taya APC magudi

Jawabin yace, "Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya aika sakon jinjina da shahidan yakin basasa wadanda suka sadaukar da rayukansu domin haduwar kan wannan kasa mai girma."

"Yayin magana lokacin da ya karbi bakuncin shugaban darikar Tijjaniyar na duniya, Sheikh Muhammadul Mahy Niass, Khalifan Sheikh Ibrahim Niass, shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga darikar bisa addu'o'insu wajen kawo karshen yakin."

"Buhari ya ce a watanni 30 da akayi yakin basasa, an yi rashin rayukan yan Najeriya kuma ya yi addu'an kada mu sake ganin irin wannan yaki."

A cewar Garba Shehu, Buhari ya yi maraba ga Khalifan kuma ya jinjinawa kokarin da sukeyi wajen kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari a halin yanzu yana ganawa tare da shugaban kasar Jamhuriyar Chadi, Idriss Deby a fadar shugaban Najeriya da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaba Deby ya isa gidan gwamnatin misalin karfe 12.15 na rana kuma mai masaukin baki, Shugaba Muhammadu Buhari ya tarbe shi inda ya gabatar da wasu yan fadarsa gare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel