Lamari Ya Kacame da ADC Ta Ce a Fitar da Ƴan Takarar Gwamna 2 a Kaduna
- Rikici ya ɓarke a jam'iyyar ADC reshen Kaduna bayan shugabannin kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafe sun ayyana mutane biyu a matsayin ɗan takarar gwamna
- Dr. Muhammed Mustapha Fagge ya tabbatar da Shuaibu Idris Mikati a matsayin wanda ya lashe tikitin gwamna kuma wanda zai yi wa ADC takara a jihar Kaduna
- Amma a gefe guda kuma, Sakataren kwamitin, Dr. Mikailu Ibrahim Barau, ya ce Hon. Isa Ashiru ne halastaccen ɗan takarar jam'iyyar da zai wakilce su a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Jam'iyyar ADC a jihar Kaduna ta shiga wani sabon rikici bayan shugabannin kwamitin sauraron korafe-korafen zaben fitar da gwani sun bayyana mutane biyu daban-daban a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar.
Shugaban kwamitin, Dr. Muhammed Mustapha Fagge, ya sanar da cewa Shuaibu Idris Mikati ne ya zama ɗan takarar gwamna bayan kwamitin ya yi nazari kan ƙorafe-ƙorafe, hujjoji da takardun da masu neman takara suka gabatar.

Source: Twitter
Jaridar The Sun ta wallafa cewa Dr. Fagge ya ce kwamitin ya amince da nasarar Mikati ne bayan tabbatar da cewa ya samu mafi yawan ƙuri'un da aka kaɗa cikin sahihanci.
Kwamitin ADC ya amince da Mikati a Kaduna
Daily Trust ta kawo labarin cewa Dr. Fagge ya ce binciken da aka gudanar ya gano wasu kura-kurai da zarge-zargen magudi da suka shafi wasu daga cikin masu neman tikitin gwamna, lamarin da ya ƙarfafa matakin tabbatar da nasarar Mikati.
Hakazalika, kwamitin ya amince da nasarar Tukur Salisu Kakeyi a mazaɓar Zariya ta tarayya da kuma Muhammed Mahmoud Aliyu a mazaɓar Soba bayan tabbatar da cewa su ne suka samu mafi yawan ƙuri'u.

Source: Original
Sai dai kwamitin ya soke sakamakon wasu zaɓukan fitar da gwani tare da umartar sake gudanar da zaɓe a wasu mazaɓu bayan gano kura-kurai, karya ƙa'idoji da kuma rashin isassun hujjojin cewa an gudanar da zaɓe yadda ya kamata.
Daga cikin wuraren da aka ba da umarnin sake zaɓe akwai Ikara/Kubau da Kaduna ta Kudu, yayin da za a sake gudanar da zaɓe a wasu gundumomi da mazaɓu domin kare sahihanci da mutuncin tsarin zaɓen jam'iyyar.
Kan kwamitin ADC ya rabu a Kaduna
Sai dai a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar ADC da ke Kaduna, Sakataren kwamitin, Dr. Mikailu Ibrahim Barau, ya ce Hon. Isa Ashiru ne halastaccen ɗan takarar gwamna na jam'iyyar.
Barau ya bayyana cewa sakamakon da kwamitin zaɓe ya tattara ya nuna Ashiru ne ya yi nasara, yana mai cewa:
"Hon. Isa Ashiru ya ci gaba da kasancewa wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna kuma ɗan takarar ADC a Kaduna."
Ya bukaci hedikwatar jam'iyyar ta ƙasa ta yi watsi da abin da ya kira "sanarwar Abuja", tare da kafa sabon kwamitin ɗaukaka ƙara domin gudanar da aiki cikin gaskiya da adalci.
ADC ta samu karuwa a Kaduna
A baya, kun samu labarin cewa jam'iyya mai mulki ta APC na ci gaba da rasa wasu 'ya'yanta yayin da ADC ke shirin tarkato kawunan 'yan adawa gabanin 2027 don a kwace gwamnati.
Daya daga cikin hadimin Uba Sani na Kaduna Hon. Yusuf Umar Garkuwa ya yi murabus daga mukaminsa tare da mika shaidarsa na zama dan jam'iyya yayin da ya ke shirin haduwa da ƴan adawa.
Ya kara da cewa cewa matakin da ya dauka ba na gaggawa ba ne, illa dai sakamakon abin da ya kira bukatar sabuwar tafiyar siyasa tare da yin dogon nazari a kan makomarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


