Gwamnati Ta Gyara Zargin da ake Yi wa Tukur Mamu kan Hada Kai da Boko Haram
- An sake gurfanar da Tukur Mamu da ake zargin an hada baki da shi wajen sace matafiya a kotun tarayya da ke Abuja kan sababbin tuhume-tuhume
- Gwamnatin tarayya na zarginsa da karɓar kasonsa na kuɗin fansa da kuma hulɗa da ƙungiyar Boko Haram a sace matafiya a jirgin kasan Abuja-Kaduna
- Mamu ya musanta dukkannin zarge-zargen da ake masa, yayin da kotu ta ɗage shari'ar bayan an gyare tsofaffin tuhume-tuhumen da ake yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sake gurfanar da Tukur Mohammed Mamu, wanda ake zargi da shiga tsakani tsakanin 'yan ta'adda da iyalan mutanen da aka sace a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kadun.
Gwamnati ta mayar da shi gaban kotun ne a kan sababbin tuhume-tuhume 17 da suka shafi laifuffukan ta'addanci da suka hada da hada kai da 'yan Boko Haram.

Source: Facebook
The Nation ta kawo labarin cewa an sake gurfanar da Mamu ne a ranar Litinin a gaban Mai Shari'a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Dalilin gyara tuhume-tuhumen Tukur Mamu
A ruwayar jariidar Vanguard, a lokacin da aka karanta masa sababbin tuhume-tuhumen, Tukur Mamu ya musanta dukkannin zarge-zargen da ake masa.
Lauyan masu gabatar da ƙara, David Kaswe, ya bayyana cewa an yi gyaran tuhume-tuhumen ne domin su dace da hujjojin da aka gabatar a gaban kotu tun bayan fara shari'ar.
Lauyan Mamu, Johnson Usman (SAN), bai yi adawa da buƙatar a karanta wa wanda yake karewa sabbin tuhume-tuhumen ba.

Source: Facebook
A cikin tuhume-tuhume daban-daban, gwamnati ta zargi Mamu da taimakawa ƙungiyar Boko Haram a kusa da watan Maris na shekarar 2022 a Kaduna.
Haka kuma ana zarginsa da ƙarfafa 'yan ta'addan su ƙi tattaunawa da kwamitin Babban Hafsan Tsaro (CDS) da gwamnati ta kafa domin sasanta sakin fasinjojin da aka sace a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.
Masu gabatar da ƙara sun ce hakan ya ba shi damar taka muhimmiyar rawa wajen karɓa da isar da kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sauran zarge-zargen da ake wa Mamu
A wata tuhuma, gwamnati ta ce Mamu ya karɓi Dala 120,000 a madadin ƙungiyar ta'addanci daga hannun iyalan waɗanda aka sace.
Ana kuma zarginsa da yin mu'amala da kuɗaɗen da ake alaƙantawa da ta'addanci da suka kai Dala 269,200 da kuma Naira miliyan 25.69 da aka ce an samu a hannunsa.
Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da mallakar wasu kuɗIn ƙasashen waje da suka haɗa da rupee 1,840 na Indiya, fam 1,700 na Masar da Dirham 115 na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Baya ga haka, gwamnatin tarayya ta zarge shi da laifuffukan halasta kuɗin haram da suka shafi Naira miliyan 25.69 da Dala 269,200.
Ana zargin Mamu da mallakar bindiga da harsasai 47 ba tare da sahihin lasisi ba, abin da ya saɓa wa dokar mallakar makamai ta Najeriya.
Hukuncin kotu game da Tukur Mamu
A baya, mun kawo labarin cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar da Tukur Mamu ya yi na a mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje bayan zargin da ake masa.
Mai shari'a Inyang Ekwo shi ne ya yi fatali da buƙatar Tukur Mamu wanda gwamnatin tarayya ke zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci, amma mai shari'ar ya umarci DSS da ta riƙa bari yana ganin likitansa.
Daga nan ne alƙalin ya umarci Tukur Mamu da ya ci gaba da zama a hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS a duk tsawon lokacin da za a kwashe kan shari’ar da ake yi masa na zargin ta'addanci
Asali: Legit.ng


