Peter Obi Ya Yabi Tinubu kan Zuwa Benue, Ya Bukaci Shugaban Kasa Ya Ziyarci Neja

Peter Obi Ya Yabi Tinubu kan Zuwa Benue, Ya Bukaci Shugaban Kasa Ya Ziyarci Neja

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa shawarar kai ziyara Benue bayan kisan gillar da aka yi
  • Sai dai Obi ya bukaci shugaban kasar da ya kai irin wannan ziyarar zuwa Mokwa, jihar Neja, inda sama da mutum 200 suka mutu sakamakon ambaliya
  • Ya ce a irin wannan yanayi ba wai juyayi na nesa kadai ya kamata ba, ya kamata a ziyarce su ne kai tsaye don tausayawa al’ummar da abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana jin dadinsa kan yunkurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kai ziyara zuwa jihar Benue.

Shugaban kasa Bola Tinubu zai kai ziyara ne domin jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Peter Obi ya yabawa Tinubu kan zuwa Benue
Peter Obi ya yabawa Tinubu kan zuwa Benue bayan kai hari. Hoto: Mr Peter Obi|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, Obi ya bukaci shugaban kasar da ya kara azama wajen kai irin wannan ziyarar zuwa jihar Neja, musamman garin Mokwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mummunar ambaliyar ruwa ce ta faru a Mokwa kuma ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 200 tare da batan fiye da mutum 1,000.

Maganar Obi kan masifar Benue da Mokwa

Obi ya ce abin da ya faru a Benue da Mokwa alama ce ta tabarbarewar lamura sakamakon rashin matakin gaggawa daga gwamnati.

A cewarsa:

“Mutane sama da 200 sun mutu a Mokwa, fiye da 1,000 kuma sun bata. Waɗannan ba kididdigar lambobi ba ce, rayuka ne na al’ummar da abin ya rutsa da su.”

Ya ce idan shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya iya yin zirga-zirgar fiye da kilomita 1,800 don jajanta wa ‘yan ƙasa fiye da 100 da suka mutu, to Tinubu ya fi kusa da Benue da Mokwa.

Ambaliya ta rusa gidaje a Mokwa
Yadda ambaliya ta rusa gidaje a Mokwa. Hoto: Yax Mokwa
Asali: Facebook

Obi ya nemi Tinubu ya dauki mataki kai tsaye

Peter Obi ya ce bai kamata a rika shugabanci daga nesa ba, ya ce akwai bukatar a rika shugabanci da zai nuna tausayi da matsawa kusa da mutane.

Obi ya ce irin salon shugabancin zai tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa suna da muhimmanci kuma gwamnati na kula da su.

“Ziyararka zuwa Mokwa za ta isar da sako mai karfi cewa rayuwar kowane dan Najeriya na da daraja, a kowane yanki yake,”

Ya kuma bukaci shugaban kasa da ya kara kaimi wajen daukar matakan tsaro, musamman a yankunan da ke fuskantar iftila’i.

Obi ya ce a irin wannan lokaci, ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen rage aukuwar irin wadannan bala’o’i ta hanyar samar da matakan dakile iftila’i.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta hada kai da gwamnatocin jihohi wajen daukar matakan gaggawa da shirya hanyoyin magance irin wannan bala’i a nan gaba.

An yi wa 'yan Benue ta'aziyyar kashe kashe

A wani rahoton, kun ji cewa kashe mutane sama da 200 a jihar Benue na cigaba da daukar hankalin 'yan Najeriya.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan tare da kira a dauki matakin da ya dace kan kashe kashe.

A daya bangaren, Sanata Abubakar Bukola Saraki da Sheikh Isa Ali Pantami sun nuna damuwa tare da kira na musamman ga gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng