'Yan Najeriya su guji tada wani yakin basasa - Yakubu Gowon

'Yan Najeriya su guji tada wani yakin basasa - Yakubu Gowon

- Tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon yayi Allah wadai da irin kisan gillar da ake yi a cikin kasar nan, sannan kuma ya gargadi 'yan Najeriya da su guji kara taso da yakin basasa

- Gowon wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 1967 zuwa 1970, yace gaskiya kashe - kashen da ake yi a kasar nan yana tada mishi hankali matuka, inda ya bayyana kashe - kashen a matsayin rashin imani da tausayin dan adam

'Yan Najeriya su guji tada wani yakin basasa - Yakubu Gowon
'Yan Najeriya su guji tada wani yakin basasa - Yakubu Gowon

Tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon yayi Allah wadai da irin kisan gillar da ake yi a cikin kasar nan, sannan kuma ya gargadi 'yan Najeriya da su guji kara taso da yakin basasa. Gowon wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 1967 zuwa 1970, yace gaskiya kashe - kashen da ake yi a kasar nan yana tada mishi hankali matuka, inda ya bayyana kashe - kashen a matsayin rashin imani da tausayin dan adam.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kai hari Masallaci

Janar Gowon yayi wannan kira ne a lokacin daya kai ziyara ga Gwamnan Imo Rochas Okorocha fadar shi dake birnin Owerri babban birnin jihar a ranar Asabar dinnan, inda yace 'yan Najeriya suna bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali, saboda hakan shine kawai zai saka al'umma ta zama daya sannan kuma a fara gabatar da ayyukan cigaba ga kasa.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na Rochas Okorocha ya fitar, Sam Onwuemeodo, ya bayyana cewar tsohon shugaban kasar yace, idan mutane suka dage da addu'a Allah zai iya kawo sauki sannan kuma ya shiryi wadanda suke aikata kashe - kashen, inda ya kara da cewa babu wani yanayi da zai gagari Allah.

Gowon yace, "Bayan yakin basasa da aka yi a shekarun baya, mun zo wannan gari na Owerri, sannan mun ziyarci Nsukka, Enugu, Abakeliki, Umuahia, da Onitsha. A lokacin munji dadin ganin yanda jama'a suka tarbe mu, suna cewa mune shugabannin su, don haka kada mu bari wasu su sha irin wahala da suka sha."

Da yake jawabi, Gwamnan jihar ta Imo Rochas Okorocha ya shawarci 'yan Najeriya dasu dauki matsala irin ta Boko Haram a matsayin matsalar kasa baki daya, kuma matsalar tana bukatar gudunmawar kowa da kowa domin kawar da ita. Yace bai kamata a maida matsalar tsaro harkar siyasa ba, inda ya kara da cewa mutane daga kabilu kala-kala sun rasa rayukan su saboda matsalar rashin tsaro da ake fama dashi a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel