Wanene tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon?

Wanene tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon?

- A rana irin ta yau Yakubu Gowon ya ke bikin kara shekara a Duniya

- Janar Gowon mai ritaya shi ne shugaba na uku da aka yi a Najeriya

- Janar Yakubu Gowon ya cika shekara 85 da haihuwa a yau Litinin

A yau 19 ga watan Oktoba, 2020, Janar Yakubu Gowon ya cika shekara 86 da haihuwa. Yakubu Gowon ya taba rike mulkin Najeriya na shekaru tara.

Legit.ng Hausa ta kawo maku takaitaccen tarihin Yakubu Gowon wanda aka haifa a shekarar 1934.

1. Iyaye da haihuwa

Ainihin iyayen Yakubu Gowon mutanen Angas ne a kasar Filato a taskiyar Najeriya. Daga baya mahaifansa, Nde Yohanna da Matwok Kurnyang su ka kaura zuwa garin Wusasa a Zariya.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa sun sa ranar da za su amince da kasafin kudin 2021

2. Girma da karatu

Gowon ya tashi ne a Zariya, jihar Kaduna, a nan ya soma karatun boko. Gowon ya na cikin wadanda su ka kware wajen harkar wasanni a lokacin da ya ke makaranta.

A shekarar 1954 aka kaddamar da Gowon a matsayin sojan kasa, ya na da shekara 21 rak.

Daga nan ya tafi makarantar sojoji na Royal Military Academy Sandhurst, Ingila. Bayan nan ya samu hoto a Staff College, Camberley, da kuma Joint Staff College, Latime.

3. Juyin-mulki

A shekarar 1966 aka hambarar da mulki a karon farko a Najeriya, daga nan Gowon ya zama shugaban hafsun sojin kasa a karkashin tsohon shugaba Jonathan Aguiyi-Ironsi.

4. Shugaban kasa

A tsakiyar 1966 aka sake kifar da gwamnati a Najeriya, wannan ya sa Janar Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa ya na da shekara 31, abin da ba a taba gani a tarihin kasar.

KU KARANTA: Ibo za su hada-kai da Arewa domin samun mulki a 2023

Wanene tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon?
Buhari da Yakubu Gowon Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

5. Yakin basasa

Gowon ya na kan mulki ne rikici ya barke, wanda hakan ya yi sanadiyyar yakin basasa da Biyafara. Bayan kusan shekaru uku a shawo kan lamarin, Najeriya ta sake dinkewa a 1970.

6. Hambarar da gwamnati

A 1975 ne aka kifar da gwamnatin Yakubu Gowon bayan ya yi shekaru kusan tara a kan mulki. Daga nan shugaban ya tsaya a kasar waje ya kara karatu, har ya samu Digirin PhD.

7. Iyali

A shekarar 1969 Gowon ya auri sahibarsa, Miss Victoria Zakari. Janar Gowon ya hau kan mulki ne ya na gwauro. An yi auren a cocin Cathedral Church of Christ da ke Legas.

A baya kun ji cewa gamayyar kungiyoyi fiye da 20 a Najeriya su na rokon a canza manyan Sojoji. Kungiyoyin masu zaman kansu, su na so a fatattaki shugabannin tsaro.

Tun a karshen shekarar 2015 aka nada Janar Tukur Buratai da sauran takwarorinsa a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel