Tashin Hankali: Uwar Gida Ta Hada Kai da Kanin Miji, Ta Kashe Jaririn Kishiyarta

Tashin Hankali: Uwar Gida Ta Hada Kai da Kanin Miji, Ta Kashe Jaririn Kishiyarta

  • Rundunar ƴan sandan Kaduna ta kama Zaliha Shuaibu bisa zargin kashe jaririn kishiyarta, ta hanyar ciyar da shi guba da shake wuyansa
  • An bayyana cewa Zaliha ta amsa laifin tare da cewa ta haɗa kai da Lawal Muhammad, ƙanin mijinta, wanda ya samo mata gubar
  • Kwamishinan 'yan sandan Kaduna, Rabiu Muhammad ya ce za a tabbatar da adalci, kuma duk masu hannu a kisan za su fuskanci hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – Rundunar ƴan sandan Kaduna ta kama wata mata mai suna Zaliha Shuaibu bisa zargin kashe jaririn kishiyarta dan wata uku a garin Malari da ke Soba.

An rahoto cewa lamarin ya faru ne ranar 13 ga Mayun, 2025, a gidan da matar ke zaune tare da mijinta da kuma mahaifiyar jaririn da aka kashe.

'Yan sanda sun cafke wata mata da ake zargin ta kashe jaririn kishiyarta a Kaduna
Shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, Mansir Hassan, ya fitar a ranar Juma’a, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uwar gida ta kashe jaririn kishiyarta a Kaduna

Mansir Hassan ya bayyana cewa Maryam Ibrahim, kishiyar Zaliha, ta bar ɗanta a ɗaki yayin da ta shiga banɗaki, amma da ta dawo sai ta tarar da Zaliha na rike da jaririn.

Lokacin da Zaliha ta mayar mata da jaririn, sai ta fahimci cewa bakinsa na fidda kumfa, kuma akwai rauni a wuyansa, wanda daga baya ya yi sanadin mutuwarsa.

Kakakin 'yan sandan ya ce:

“Binciken farko ya nuna cewa Maryam Ibrahim ta bar ɗanta ɗan wata uku a ɗaki, inda Zaliha ta shiga ta ɗauke shi. Da ta dawo, sai ta tarar da kishiyarta na rike da shi.

Kanin miji na da hannu a kashe jaririn yayansa

Ya kara da cewa:

“Bayan ta karɓi jaririn, sai ta lura bakinsa na fitar da kumfa, sannan akwai rauni a wuyansa. An garzaya da shi asibitin ƙauyen, inda aka tabbatar da mutuwarsa.”

Mansir Hassan ya ce bincike ya tabbatar da cewa Zaliha ce ke da hannu a kisan, kuma ta haɗa kai da ƙanin mijinta, Lawal Muhammad, wanda yanzu ake nemansa.

Zaliha ta amsa laifin cewa ta yi amfani da guba wajen kashe jaririn, kuma Lawal ne ya samo mata gubar da ta ba yaron.

An cafke wata mata da ta kashe jaririn kishiyarta ta hanyar ciyar da shi guba a Kaduna
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kaduna a Arewa ta Tsakiya. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zaliha ta amsa laifin kashe jaririn kishiyarta

Sanarwar Mansir ta nuna cewa:

“Bayan da abin ya faru, DPO na Soba ya gudanar da bincike cikin gaggawa inda aka kama Zaliha Shuaibu.
"Lokacin da aka yi mata tambayoyi, ta amsa laifin tare da bayyana cewa ta haɗa baki da Lawal Muhammad, ƙanin mijinta, wanda har yanzu ba a gan shi ba.
"Zaliha ta shaida wa 'yan sanda cewa Lawal ne ya samo mata gubar da ta yi amfani da ita wajen aikata wannan danyen aiki."

Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna, Rabiu Muhammad, ya ce za a tabbatar da adalci, kuma duk wanda aka samu da hannu a lamarin zai gurfana a gaban kotu.

Yadda mata ta kashe jaririn kishiyarta a Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sandan Katsina sun kama wata mata mai suna Aisha Abubakar bisa zargin kashe ‘yar mijinta ta hanyar bata guba.

An ce Aisha Abubakar ta bai wa yarinya ‘yar shekara huɗu abinci da aka zarga ya ƙunshi guba, a Sabuwar Unguwa Kwatas, karamar hukumar Rimi.

Bayan zurfafa bincike, Aisha Abubakar ta amsa laifinta, tana mai cewa kiyayyar da take wa mahaifiyar yarinyar ce ta saka ta aikata wannan danyen aikin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.