'Akwai Hadari:' Amnesty Int'l Ta Soki Shirin Mika Hamdiyya ga Yan Sanda

'Akwai Hadari:' Amnesty Int'l Ta Soki Shirin Mika Hamdiyya ga Yan Sanda

  • Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta soki shirin mayar da Hamdiyya Sharif ga ‘yan sandan Sakkwato maimakon bata kulawar likita
  • Amnesty Int'l ta ce rayuwar matashiyar na cikin haɗari, kuma ta bukaci gwamnati ta kare lafiyarta da ‘yancinta ba tare da mika ga Sakkwato ba
  • Gwamnatin Sakkwato na tuhumar Hamdiyya da tayar da zaune tsaye bayan bidiyon da ta soki yadda ake magance matsalar tsaro a jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Amnesty Int'l a Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da hukumomi ke shirin ɗauka na mayar da Hamdiyya Sharif.

Hukumomi sun bayyana cewa za su mika Hamdiyya ga hannun jami’an ‘yan sanda, maimakon bata damar samun kulawa da ta dace da halin da take ciki.

Hamdiyya
Ana fargabar mika Hamdiyya ga jami'an Sakkwato Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

A hirarsa da BBC, Shugaban Amnesty International a Najeriya, Mallam Isa Sanusi, kwamishinan ‘yan sandan Zamfara ya ce za su mayar da Hamdiyya Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amnesty Int'i na son a kai Hamdiyya asibiti

A cewar Mallam Isa Sanusi, tun da farko sun dauka cewa za a mika ta ga kwararrun likitoci domin samun kulawa ta musamman, wanda shi ne ya fi dacewa da ita a halin yanzu.

“Mu yanzu abin da muka fahimta a taƙaice shi ne kenan an kamata, ko kuma sun riƙe ta,” in ji shi.

Rahotanni sun ce an gano Hamdiyya Sherif ne a wani ƙauye da ke cikin jihar Zamfara da yammacin Laraba, bayan da aka yi ta nemanta tun daga ranar Talata a jihar Sakkwato.

Halin da Hmadiyya Sherif ke ciki

Wata daga cikin danginta ta bayyana cewa wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da Hamdiyya, sannan suka yi mata wata allura da ta sanya ta fita hayyacinta.

Shugaban Amnesty International ya jaddada cewa:

“Yanzu haka rayuwar Hamdiyya Sharif na cikin haɗari, kuma wajibi ne hukumomin Najeriya su ba ta kariya.”

Matashiyar na fuskantar shari’a a Sakkwato, inda gwamnatin jihar ke zarginta da laifin tayar da zaune tsaye.

Hamdiyya
An tsinci Hamdiyya a cikin mawuyacin hali Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

Wannan na zuwa ne bayan ta wallafa wani bidiyo da ke caccakar gwamnatin jihar bisa rashin daukar matakan da suka dace kan matsalar tsaro.

Amnesty Int'l da lauyoyin Hamdiyya sun zargi gwamnatin jihar Sakkwato da yunƙurin murkushe masu bayyana ra’ayinsu kan matsanancin halin da suke ciki.

An gano Hamdiyya Sharif

A baya, mun wallafa cewa an gano Hamdiyya Sharif, matashiyar mai fafutukar kare hakkin ɗan adam da kuma mai sukar gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu,awanni da bacewarta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an samo ta ne a Zamfara, inda aka garzaya da ita babban asibitin gwamnati na Bakura da ke jihar, ganin yadda ta fada a cikin mawuyacin hali.

Lauyanta, Abba Hikima, ya tabbatar da cewa an sace Hamdiyya ne a jihar Sakkwato lokacin da ta fita sayo kayan miya, kuma a loakcin da aka kai ta asibitin, tana tare da jami'an tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.