Yadda tsabar kishi ya saka wata mata kashe diyar kishiyarta da guba a Katsina

Yadda tsabar kishi ya saka wata mata kashe diyar kishiyarta da guba a Katsina

Hukumar 'yan sandan jihar Katsina sun cafke wata mata mai suna Aisha Abubakar mai shekaru 38 a duniya, a kan zarginta da ake da halaka 'yar mijinta ta hanyar ciyar da ita guba.

A takardar bayanin abunda ya faru wacce kakakin hukumar 'yan sandan jihar, SO Gambo Isah ya ba manema labarai a ranar Talata a Katsina.

Yace lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Nuwamba a Sabuwar-Unguwa kwatas da ke karamar hukumar Rimi a jihar.

Isah ya ce, ana zargin Aisha ne da ba wa yarinyar mais shekaru hudu a duniya, guba a cikin abinci. Tuni kuwa ta fadi rai a hannun Allah bayan da ta ci abincin.

Kamar yadda yace, yarinyar ta mutu ne bayan da aka garzaya da ita asibiti.

Ya bayyana cewa, wacce ake zargin ta amsa laifinta tare da cewa, tsanar da take wa mahaifiyar yarinyar ne ya ja hakan.

DUBA WANNAN: An kama wani tsohon kansila da laifin satar mota

Kakakin hukunar 'yan sandan yace, za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike ta yadda zata zamo aya ga sauran na baya.

Isah ya bayyana cewa, 'yan sandan sun yi nasarar kama wani Ibrahim Kasim mai shekaru 22 a Makera Funtua. Ana zarginsa da satar kanwarshi da suke uba daya.

Yace, lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Nuwamba bayan da wana ake zargin ya hada baki da budurwasa Murja wajen aikata nugun aikin.

Tuni dai 'yan sandan suka cafke wanda ake zargin tare da tseratar da Asiya mai shekaru 6.

Yace, wanda ake zargin ya kira mahaifin yarinyar a waya tare da bukatar kudin fansa har naira miliyan 10. Ya ce, hukumar na yin duk kokarin da ya dace don ganin ta cafke sauran 'yan kungiyara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel