An Yi Rashi: Dan Najeriya Ya Rasa Ransa yayin Taya Rasha Yaki da Ukraine

An Yi Rashi: Dan Najeriya Ya Rasa Ransa yayin Taya Rasha Yaki da Ukraine

  • Hukumomi a kasar Ukraine sun sake sanar da mutuwar wani ɗan Najeriya yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin kasar da Rasha
  • Rahoton ya bayyana cewa marigayin ɗan jihar Ondo ne, kuma ya shiga aikin soja bayan an gargadi ’yan Najeriya kan shiga yaƙe-yaƙen
  • Hukumomin Ukraine sun ce akalla ’yan Najeriya 215 sun shiga aikin soja da Rasha, yayin da sama da mutum 25 suka mutu ko suka ɓace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kiev, Ukraine - Hukumomi a kasar Ukraine ta bayyana mutuwar wani ɗan Najeriya mai suna Ayebusiwa Olabode Victor.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ana zargin yana yaƙi tare da dakarun Rasha a yaƙin Ukraine domin taimaka mata.

An kashe dan Najeriya a yakn Rasha da Ukraine
Shugaba Bola Tinubu na Najerya ya y tagumi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hukumar leƙen asirin tsaron Ukraine ta ce Victor an haife shi ranar 28 ga Afrilu, 1992, kuma ya fito daga Ilutitun a jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ministan tsaro ya bayyana yadda aka yaudari kananan sojoji

Ana daf da kawo karshen yakin Rasha, Ukraine

Wannan na zuwa yayin da hukumomi a kasar Ukraine suka bayyana cewa ana shirin tsagaita a yakin da ake da ake yi tsakaninta da Rasha.

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun sojojin Rasha da Ukraine bayan fiye da shekaru hudu ana gwabza fada.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi tsokaci kan lokacin da za a kawo karshen yakin wanda ya jawo asarar rayuka masu yawa.

Yadda aka kashe dan Najeriya a yakin Rasha

Rahoton ya nuna cewa an kashe Victor ne a yankin Kharkiv kusa da garin Hrafske yayin da ake ci gaba da yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine.

Ukraine ta ce Victor ya rattaba hannu kan kwangilar aikin soja a ƙarshen watan Fabrairu bayan gargadin Najeriya kan ɗaukar mayaƙa ba bisa ƙa’ida ba.

Tun kafin wannan sanarwa, Ukraine ta ce ta gano gawar wasu ’yan Najeriya biyu a yankin Luhansk waɗanda ake zargin suna yaƙi a gefen Rasha.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Hukumomin Ukraine sun ce akalla ’yan Najeriya 215 sun shiga aikin soja na Rasha, yayin da mutum 25 suka mutu ko suka ɓace a yaƙin.

Tun kafin wannan sanarwa, Ukraine ta ce ta gano gawar wasu ’yan Najeriya biyu a yankin Luhansk waɗanda ake zargin suna yaƙi a gefen Rasha.

Hukumomin Ukraine sun ce akalla ’yan Najeriya 215 sun shiga aikin soja na Rasha, yayin da mutum 25 suka mutu ko suka ɓace a yaƙin.

An kashe yan Najeriya 4 a yakin Rasha

A baya, mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun an kashe ‘yan Najeriya hudu da aka dauka aiki a Rasha bayan an tura su fagen yaki a Ukraine yayin da ake ci gaba da gwabza fada.

Rahotanni sun ce an yaudare su da tayin za a ba su aikin tsaro kafin a tilasta masu shiga aikin soja bayan sun isa kasar.

Iyalan mamatan sun ce ba a taba tuntubar su daga hukumomin Rasha ba duk da an kashe masu 'yan uwa a fagen daga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.