ADC: Hadakar Su Atiku Ta Karyata Zaben Jam'iyyar da za a Taru don Kayar da Tinubu
- Hadakar Atiku Abubakar ta nesanta kanta daga rahotannin cewa ta amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin takararta a zaben 2027
- Ta bayyana cewa ana ci gaba da laluben jam'iyyar da za a yi amfani da ita wajen tabbatar da APC ba ta koma mulki ba bayan babban zabe mai zuwa
- Mai magana da yawun hadakar, Salihu Moh. Lukman ya zargi wasu da kokarin tayar da husuma a tsakanin jagororin tafiyar saboda son zuciya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hadakar siyasa da Atiku Abubakar ke jagoranta ta nesanta kanta daga rahotannin da ke cewa ta zabi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za ta yi amfani da shi a zaben 2027.
Wani jigo a cikin hadakar, Salihu Moh. Lukman, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, inda ya zargi bata-gari da yada labarin karya.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Lukman, tsohon 'dan kwamitin gudanarwa na kasa na APC, ya karyata rahoton da ke cewa an nada shi a matsayin shugaban ofishin hadakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Ba mu zabi ADC ba,’ Hadakar Atiku
Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Salihu Moh. Lukman ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton, yana mai cewa karya ce tsagwaronta.
A cewarsa, tattaunawa na ci gaba da gudana tsakanin shugabannin hadakar, kuma sanarwar za ta fito daga jagororinta idan an cimma manufa.

Asali: Facebook
Sanarwar ta ce:
"Hankalina ya kai ga rahoton cewa an nada ni shugaban ofishin hadakar Atiku. Jama’a su yi watsi da wannan labari domin ba gaskiya ba ne. Ba a yanke irin wannan hukunci ba."
"Haka zalika, labarin da ke cewa hadakar ta zabi ADC a taron da aka yi a ranar Talata, 20 ga Mayu, 2025, karya ce."
Hadakar Atiku ta soki 'yan adawa
Salihu Moh. Lukman ya zargi wasu ‘yan adawa da kokarin yada jita-jita game da zaben jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da hadakar Atiku za ta yi amfani da shi.
Lukman ya ce:
"Abin takaici, wasu masu son kawo rudani suna yada labaran bogi da nufin kawo sabani a tsakanin shugabannin hadakar."
"Muna kira ga jama’a da kafafen yada labarai da su yi watsi da irin wadannan labaran karya da son zuciya."
Atiku da Obi sun magantu kan hadaka
A baya, mun wallafa cewa tsofaffin ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, sun karyata cewa sun cimma manufa a kan hadakar adawa.
Wani rahoto da ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da wasu jaridu ya yi zargin cewa Atiku ya miƙa tayin kujerar mataimaki ga Peter Obi domin a hada kai gabanin zaben 2027.
Atiku, wanda ya musanta batun ya ce a ce duk wata ganawa da ake yi tsakaninsu da sauran jiga-jigan ‘yan adawa na da nufin samar da wata sabuwar kafa mai ƙarfi da za ta ceto Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng