Na kashe jaririn kishiya na bisa kuskure ne, Inji Rabi'atu
- Wata mata mai suna Rabi'atu Nura tayi sanadiyyar mutuwar jaririn kishiyar ta mai kwanaki 40 a duniya
- Rabi'atu tace ta baiwa yaron ruwan sha ne alhalin hannun ta ya taba gubar bera ba da sannin ta ba
- An kai jaririn asibiti inda aka bashi magani amma daga baya yace ga garinku
Jami'an rundunar yan sanda na Jihar Katsina sun tsare wata mata mai suna Rabi'atu Nura wadda ke zaune a garin Mazoji da ke karamar hukumar Mai'addua na Jihar Katsina bisa zargin kashe jaririn kishiyan ta.
Rahotanni sun ce matar ta baiwa yaron guba ne cikin ruwan sha wanda yasa jaririn ya fara amai kuma aka garzaya dashi zuwa asibiti da babban asibiti da ke Daura inda aka bashi magani, sai dai jim kadan bayan an dawo dashi gida, jaririn yace ga garin ku.
Rabi'atu tace ta baiwa yaron ruwan sha alhalin bata san cewa ta taba maganin bera ba wadda hakan ne yayi dalilin mutuwar jaririn mai kwanaki 40 a duniya.
DUBA WANNAN: Sarkin Kano ya zargi su babba da jaka bisa halin tabarbarewar arzikin Najeriya
Rabi'atu tace suna zaman lafiya da uwar jaririn har ma ta yafe mata amma iyayen kishiyar sun ce dole sai hukuma ta dauki mataki akan lamarin.
Hukumar yan sanda na cigaba da gudanar da bincike, kuma sun kara da cewa nan da lokacin kadan za'a gurfanar da Rabiatu gaban kotu bisa laifin kisa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng