Yaki da Badala: Hisbah Ta Shiga Otel a Sokoto, Ta Kama Maza da Mata

Yaki da Badala: Hisbah Ta Shiga Otel a Sokoto, Ta Kama Maza da Mata

  • Rahoto ya nuna cewa Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta kai samame wasu yankuna, inda ta kama mutane sama da 10 a otel daban-daban
  • Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta kaddamar da shirin Operation tsaftace birnin Shehu domin kawar da badala da alfasha a jihar Sokoto
  • Mutane sun yi martani game da samanen, wasu na cewa ya yi daidai suna kara bayar da bayanai game da wasu wurare, wasu kuma na suka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto karkashin jagorancin Imam Surajo Abubakar ta kai samame wasu otel guda uku da ke jihar.

Rahotanni sun nuna cewa sama da maza da mata 10 ne dakarun hukumar Hisbah suka kama a samamen, kuma bincike na cigaba da gudana a kansu.

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

Jami'an Hisbah a jihar Sokoto
Jami'an hukumar Hisbah a bakin aiki a Sokoto. Hoto: Sokoto State Hisbah Board
Source: Facebook

Legit Hausa ta samu bayanai game da samamen da Hisbah ta kai ne a wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Hisbah ta kai samame a Sokoto

Yayin da Hisbah ke cigaba da kokarin yaki da badala a jihar Sokoto, jami'an hukumar sun cafke mutane 16 a wasu otel-otel.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna cewa:

"Da yammacin ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2026, hukumar Hisbah ta jihar Sakoto ta kai wani samame a wasu manyan otal-otal guda uku da ke cikin birnin Sokoto.
"Otal-otal din sun hada da Pinnacle, Duniya Hotel da Ifoma, inda aka cafke mutane 16, maza da mata.

Yayin bayani kan wanda ya jagoranci samamen, Hisbah ta ce:

"Wannan samame ya gudana ne karkashin jagorancin mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Sakoto, Imam Surajo Abubakar."
"An gudanar da wannan aiki ne a karkashin shirin Operation Tsaftace Birnin Shehu."

Kara karanta wannan

Bayan batun takarar Fubara, kotu ta rusa jagororin APC da ke wa Wike biyayya

Ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya

'Yan Najeriya, musamman mazauna Sokoto, sun bayyana ra'ayoyi game da samanen Hisbah, inda Abubakar Usman Binji ya ce:

"A gaskiya aikin da Hisbah ke yi akwai wasu kura-kurai a cikinsa. A matsayinku na Musulmai, bai kamata ku rika shiga dakunan da ake aikata fasadi kuna daukar bidiyo ko hotuna ba.
"Wallahi, babu wanda bai san abin da yake yi ba daidai ba ne, amma idan ku ka zo ku ka dauke shi a bidiyo, abin zai bazu a duniya. Wannan ba daidai ba ne.
"Haka kuma, idan wanda ba Musulmi ba ya ga kuna yin haka, zai iya cewa addinin Musulunci ba addinin rufa asiri ba ne. Wannan ma ba daidai ba ne."
'Yan Hisbah yayin samame a Sokoto
Jami'an Hisbah a wani otel da suka je kama mutane a Sokoto. Hoto: Sokoto State Hisbah Board
Source: Facebook

Aminu Alhussaini Amanawa ya ce:

"Masha Allah, Hisbah na aiki.
"Don Allah mai kula da wannan shafi ya rika kula da ka'idojin rubutun Hausa, musamman yadda ake amfani da manyan da kananan harufa."

Kara karanta wannan

Matsalar ruwan sha ta yi katutu a jihar Gombe, jama'a na shan azaba

Bilal Abubakar ya ankarar da Hisba da wani waje da ya ce ana fasadi:

"Akwai wani wuri da aka bude kwanan nan mai suna Chop Life, a yankin Masallaci Uku kafin a isa ofishin Hukumar Shige da Fice. Wurin yana gaban ofishin, kuma ana aikata fasadi a can musamman da dare."

Hon. Usman Aliyu Tambuwal ya ce:

"Madallah. Sai kuma otel din Karma, Dankani, Sokoto Hotel, Shukura da Ibro. Idan ba ku je wadannan wuraren ba, to akwai siyasa a ciki."

Abdullahi Ibrahim ya ce:

"Kwarai kuwa, ku ci gaba da tsaftace birnin Sokoto. Amma kuma ku taimaka wajen rage tsadar aure da kuma riya da ake yi a cikinsa. Hakan zai taimaka wajen tsaftace birnin Sakoto.
"Sannan ai akwai manyan mutane masu gidajen baki. Idan da gaske kuke yi, ku sa ido a kansu ma."

An kori 'yan Sokoto daga gidajensu

A wani labarin, mun kawo muku cewa kuniyar Amnesty mai rajin kare hakkin dan Adam ta bayyana cewa 'yan ta'adda na korar mutane a gidajensu a Sokoto.

Kara karanta wannan

Masu POS sun fara barazanar dakatar da aiki a Najeriya

Hakan na kunshe a wata sanarwa da kungiyar ta fitar, inda ta ce 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun addabi Sabon Birni da Isa.

Amnesty ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma a dukkan birane da kauyukan kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng