'Tinubu Ya Cancanci Tazarce saboda Dukufa kan Magance Rashin Tsaro,' APC
- Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya soki manufofin shugaba Bola Tinubu, inda ya ce ba su kawo cigaba ba
- Adebayo ya daura alhakin rashin magance kalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da matsalar tsaro, kan gwamnatin Tinubu
- Sai dai kakakin jam'iyyar APC na kasa, Felix Morka ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya yi aiki sosai wajen magance matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan sukar jagoran SDP ga Bola Tinubu, jam’iyyar APC ta kare manufofi da tsare-tsaren da shugaban kasar ya aiwatar tun bayan zuwan shi a 2023.
APC ta ce ya kamata ’yan Najeriya su kasance masu fata mai kyau game da makomar kasar saboda ci gaban da aka samu tun bayan hawan gwamnatin mulki a shekarar 2023.

Source: Facebook
APC ta kare Bola Tinubu
Da yake magana a shirin Sunday Politics na Channels Television, Kakakin APC na kasa Felix Morka, ya ce yanayin kasar ya canza sosai karkashin shugabancin Tinubu.
“Ina ganin ’yan Najeriya suna da dukkan dalilan da za su sa su kara amincewa da kasarsu, kuma su kasance masu kyakkyawan fata, domin idan ka kwatanta halin da kasar ke ciki a shekarar 2023 da yadda take a yau, kamar ka kwatanta dare da rana ne,”
In ji shi.
Kakakin APC ya ce tattalin arzikin da gwamnatin ta gada a watan Mayun 2023 bai da kyau sosai, yana mai nuni da tangarda a kasuwar canjin kudi da sauran bangarori.
Punch ta rahoto Morka ya ce:
“Ya zuwa watan Mayun 2023, kasar nan ba ta cikin yanayi mai kyau. Dukkan muhimman alkaluman tattalin arziki ba su daidaita ba.
“Daga canjin kudi zuwa harkokin rayuwa na yau da kullum, komai kamar yaudara ne. Yawancin abubuwan yaudara ne, kuma na ce ‘yaudara’ ne saboda ba su kasance na hakika ba, domin tangardar da ke cikin tattalin arziki ta yi yawa a kowane bangare,”

Source: UGC
APC ta yabi Tinubu kan tsaro
Game da matsalar tsaro da ta addabi Najeriya, Felix Morka ya ce ya kamata a sake zaben Tinubu a 2027 saboda yadda ya mayar da hankali kan magance matsalar 'yan ta'adda.
Morka ya kara da cewa a karkashin Bola Tinubu ne aka kashe manyan 'yan ta'adda da suka jagoranci kai hare-hare wurare da dama a kasar nan.
Ya ce:
“Ina ganin shugaba Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu saboda ya yi aiki fiye da kowane shugaban kasa da ya gabace shi wajen tunkarar matsalar tsaro.”
Gwamnan APC ya nemi afuwa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya roki al’ummar jihar da su yafe kura-kuran gwamnatinsa da na ’yan majalisarsa.
Baya ga neman afuwar al'umma, gwamnan ya mika bukata ga talakawan jihar kan su goyi bayan Jam’iyyar APC a babban zaben shekarar 2027.
Da yake jawabi, gwamnan ya ce ya amince cewa gwamnatinsa za ta iya yin yin wasu kura-kurai yayin da suke kokarin kawo wa jihar cigaba.
Asali: Legit.ng

