Gwamnatin Tinubu Ta Maka Sanata Natasha a Kotu, Akpabio, Yahaya Bello za Su Yi Shaida

Gwamnatin Tinubu Ta Maka Sanata Natasha a Kotu, Akpabio, Yahaya Bello za Su Yi Shaida

  • Godswill Akpabio da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello na daga cikin shaidu a karar da gwamnati tarayya ta kai Sanata Natasha Akpoti
  • Gwamnatin tarayya na zargin Natasha da ɓata suna da ƙage ga Akpabio da Yahaya Bello, ciki har da zargin cewa sun shirya kashe ta
  • Shari’ar na zuwa ne bayan dakatar da Sanatar Kogi ta Tsakiya daga Majalisar Dattawa, lamarin da ta alakanta da siyasa don hana ta sakat

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara a gaban kotun birnin tarayya tana zargin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da yin furucin ƙarya da ya ɓata sunan manyan jami’ai.

Ana karar Natasha da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya a shari’a mai lamba CR/297/25 wadda aka shigar a ranar 16 ga Mayu, 2025.

Natasha
Gwamnatin tarayya ta maka Natasha a kotu. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Rahoton Punch ya nuna cewa Akpabio da Yahaya Bello za su kasance cikin shaidu guda shida da gwamnatin tarayya ta jero domin bayar da shaida kan Natasha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zarge-zargen da ke cikin shari’ar Natasha

A cewar gwamnati, Natasha ta furta wasu kalamai a cikin wata hira da Channels TV a ranar 3 ga Afrilu, 2025, inda ta zargi Akpabio da Yahaya Bello da tattauna shirin kashe ta a wani taro.

Vanguard ta wallafa cewa takardar karar ta ce Natasha ta furta cewa:

“Daya daga cikin abubuwan da suka tattauna a wannan dare shi ne yadda za a kawar da ni... Akpabio ya jaddada cewa a kashe ni a Kogi,”

A wani lokaci daban a ranar 27 ga Maris, 2025, an zargi Natasha da cewa ta ce wa wata mata mai suna Sandra Duru ta waya cewa Akpabio na da hannu a satar gabobin wata mata.

An yi zargin ne a bisa cewa Natasha ta alakanta cire gabobin marigayiya Iniubong Umoren don jinya ga matar Akpabio.

Gwamnatin tarayya ta ce hakan ya karya dokokin Penal Code sashe na 391 da 392 da ke magana kan ɓata suna da cin mutunci ta hanyar ƙarya.

Akpabio zai yi shaida kan Natasha a kotu

Baya ga Akpabio da Yahaya Bello, sauran shaidu da aka jero sun haɗa da Sanata Asuquo Ekpenyong, Sandra Duru, da jami’an bincike: Maya Iliya da Abdulhafiz Garba.

Shari’ar na zuwa ne bayan Natasha ta sha alwashin cewa dakatarwar da aka mata daga majalisa a ranar 6 ga Maris na da alaka da siyasa don hana ta faɗar gaskiya.

Natasha
Akpabio zai yi shaida kan Natsha a kotu. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

Sanatar ta kai ƙarar dakatarwar a kotun tarayya inda ake sa ran za a yanke hukunci a ranar 27 ga Yuni.

Akpabio da Yahaya Bello sun rigaya da kai ƙara wajen Sufeto Janar na ‘yan sanda suna zargin Natasha da ɓata suna da tunzura jama’a.

Akpabio ya kai karar Natasha a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya maka Natasha Akpoti a kotu kan zargin rashin kunya.

Shugaban majalisar ya zargi Natasha da rashn girmama umarnim kotu kan wallafa rubutu a intanet game da shari'ar da suke yi.

A kwanakin baya kotu ta hana su rubutu ko hira da manema labarai kan shari'ar da suke yi amma Akpabio ya zargi Natasha da karya dokar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng