Zafin kishi ya sanya wata matar basarake kashe ‘yar kishiyarta
- Matar wani basarake da kawayenta sun hada baki don kashe kishiyarta
- Sai bayan cinna wuta a gidan kishiyar 'yarta ce karama ta rasu yayin da ita kuma take asibiti
- Yanzu haka idonsu ya raina fata bayan shiga hannun 'yan sanda
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun ta cafke wata matar wani basaraken gargajiya yau Alhamis tare da karin wasu mutane biyu bisa zargin cinnawa gidan kishiyarta wuta wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ‘yar kishiyar mai shekaru 3 a gabarar.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Olafimihan Adeoye ya bayyana cewa mijin wacce ake zargin wanda basaraken gargajiya ne mai suna Oba Morufudeen Olawale ne ya kai karar faruwar lamarin ga hukumar.
Oba Morufudeen dai shi ne mai rike da sarautar Alabudo a Abudo dake karamar hukumar Egbedore ta jihar Osun.
Basarake Adeoye ya ce matar tasa da ake zargi tare da wadansu abokan shedancin nata biyu ne suka baro gidajensu suka je unguwar Ede ta yankin Abudo inda gidan daya matar tasa take tare da ‘yarta takanas suka cinna wutar da misalin karfe 1:00am na dare, a ranar 6 ga watan Yunin da ya gaba ta.
KU KARANTA: Wani dan kuka ya kashe Uwarsa har lahira, hukuncin da ya biyo baya yayi dai-dai
A sakamakon hakan ne hayaki ya yiwa ‘yar yarinyar illar har ta ce ga garinku nan, yayin da ita ita kuma mahaifiyar yarinyar ta samu mummunan rauni.
Kwamishinan ‘yan sandan na jihar ya shaida cewa yanzu haka tana can asibiti tana karbar magani
Sannan ya ce binciken ‘yan sanda dai ya nuna cewa matar da ta cinna wutar ita ce matar basaraken ta uku yayin da wadda aka cinnawa gidanta wuta kuma take ta hudu.
Kuma ya ce da zarar an kammala bincike za’a mika matan uku da ake zargi domin girbar abinda suka shuka.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng