Jigon APC Ya Yi Martani ga Gwarzo, Ya Fadi Abin da zai Hana Abba Faduwa Zabe a Kano

Jigon APC Ya Yi Martani ga Gwarzo, Ya Fadi Abin da zai Hana Abba Faduwa Zabe a Kano

  • Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso ya yi martani ga tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamred Aminu AbdusSalam Gwarzo a kan Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Ya ce babu wata jam’iyyar adawa da za ta hana Gwamna Abba Kabir Yusuf sake lashe zaɓe a 2027 da ke kara karato wa duk da zafin adawa
  • Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce nasarorin da aka samu a fannoni daban-daban sun ƙara wa Gwamnan ƙarfi gabanin babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Daraktan kuɗi na Hukumar Raya Kwarin Kogin Hadejia-Jama’are (HJRBDA), Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa babu wata adawa da za ta iya hana Gwamna Abba Kabir Yusuf sake komawa kan kujerarsa karo na biyu.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar daga birnin Makkah na ƙasar Saudiyya a ranar Lahadi,3 ga watan Mayu, 2026 inda ya nuna cikakken goyon baya ga gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi darajar da zai ba Kwankwaso a matsayin mataimakinsa bayan nasararsu

Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Abba zai koma kujerar mulkin Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a wani taro a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa kalaman nasa na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun danganta da 'dan takarar gwamna a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, da cewa Gwamna Yusuf zai sha kaye a zaɓen 2027.

Jigon APC ya kare gwamnatin Abba

Rahoton ta ce Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi watsi da wannan hasashe, yana mai cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samu gagarumar nasara a kusan dukkannin muhimman fannoni na rayuwar al’umma.

Ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnan ya aiwatar da manyan ayyuka a bangarorin ilimi, lafiya, gine-ginen more rayuwa da walwalar jama’a.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa wannan lamarin da ya sanya samun wa’adin mulki na biyu ya zama abin da zai yi wuya a hana shi.

Kwankwaso ya jero nasarorin Abba a Kano

A cewar Kwankwaso, daya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Kano shi ne ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi tare da ware kusan kashi ɗaya bisa uku na kasafin kuɗin jihar ga wannan bangare.

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

Ya ce hakan ya haifar da ɗaukar malamai sama da 10,000 aiki, samar da dubunnan kujeru da tebura ga makarantu, rabon kayan makaranta kyauta da kuma bayar da guraben karatu a cikin gida da ƙasashen waje ga ɗaliban jihar.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Abba ya yi ayyuka a Kano
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Haka kuma ya ce gwamnatin ta gudanar da ayyukan gina da gyaran daruruwan kilomitoci na hanyoyi a birane da karkara, tare da aiwatar da manyan ayyukan gadoji da faɗaɗa tituna a sassan jihar.

Ya kuma yabawa ƙoƙarin gwamnati wajen magance matsalolin wutar lantarki da samar da ruwa, inda ya ce an fara rabon tiransifoma 500 tare da farfaɗo da cibiyar tace ruwan Tamburawa domin inganta samar da tsaftataccen ruwa.

Na kusa cika alkawuran da na dauka - Abba

A baya mun kawo labarin cewa gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru uku da ya yi yana mulki a jihar da gudanar da manyan ayyukan inganta rayuwa.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ya cika kusan kashi 90 cikin 100 na alkawuran da ya yi wa jama’a cikin shekaru uku da ya yi a mulki kuma ana ci gaba da wasu ayyukan a sassa daban-daban.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron Sallah da ya karɓi Sarkin Rano, inda ya ce an samu ci gaba a fannoni da dama da suka hada da ilimi da noma da sauran ababen more rayuawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng