'Ka Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Abuja,' Majalisa Ta Aika Sabuwar Buƙata ga Tinubu

'Ka Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Abuja,' Majalisa Ta Aika Sabuwar Buƙata ga Tinubu

  • Majalisar wakilai ta bukaci Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan lafiyar FCT saboda yawaitar matsaloli a cibiyoyin lafiya na gwamnati
  • Hon. Nnamdi Ezechi ya ce karancin gadaje da ma’aikatan lafiya yana haddasa mutuwar da za a iya kauce mata a asibitocin birnin Abuja
  • Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi domin gudanar da bincike kan tsarin lafiya a FCT, tare da mika rahoto da shawarwari cikin makonni huɗu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a kan tsarin lafiya na babban birnin tarayya saboda tabarbarewar da ya yi.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo sabon tsarin gina cibiyoyin lafiya na dogon zango da zai dace da yawan jama’ar da ke karuwa a Abuja.

Majalisar tarayya ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a tsarin kiwon lafiya na Abuja
Shugaba Bola Tinubu yayin da ya ke jawabi ga 'yan majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Majalisa ta kawo bukatar gyara asibitocin Abuja

Haka kuma, majalisar ta ce dole ne a saki kudin gaggawa domin inganta asibitoci, daukar karin ma’aikatan lafiya, da samar da kayayyakin aiki na zamani, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadannan matakai da majalisar ta dauka sun biyo bayan kudirin da Hon. Nnamdi Ezechi ya gabatar a zaman majalisar da aka yi jiya.

Da yake gabatar da kudirin, Hon. Ezechi ya nuna damuwa kan kalubalen da tsarin lafiya ke fuskanta a Abuja, inda ya ce babu wadatattun gadaje ko ma'aikata a asibitoci da cibiyoyin lafiya na gwamnati.

Ya bayyana cewa yawan jama’ar Abuja ya karu matuka a cikin shekaru 20 da suka gabata, yayin da yawancin asibitocin gwamnatin birnin an gina su ne tun shekaru da dama da suka wuce, ba tare da karin gini ko fadada su ba.

An fadawa gwamnati abin da ya kamata ta yi

Ya ce saboda rashin gado da yalwar wuri, marasa lafiya na kasa samun kulawar da ta cewa, abin da ya ce yake haddasa mutuwar da za a iya kauce mata.

Hon. Ezechi ya kuma bayyana cewa karancin ma’aikatan lafiya ciki har da likitoci da malaman jinya da sauran jami’an lafiya na kara tsananta lamarin.

Ya ce idan ba a dauki matakin gaggawa ba, matsalar lafiyar da ake ciki na iya rikidewa zuwa wani mummunan yanayi mai wuyar magancewa, wanda zai jefa jama’ar Abuja cikin hadari.

Majalisar wakilai ta kawo bukatar gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya na babban birnin tarayya
Zauren majalisar wakilai da ke Abuja. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisa za ta binciki fannin lafiya na Abuja

Duk da haka, ya nuna cewa idan aka gudanar da bincike da gyaran ingantattun cibiyoyin lafiya tare da daukar karin ma’aikatan lafiya, za a iya shawo kan matsalolin lafiyar.

Majalisar ta kuma bukaci ma’aikatar lafiya ta Tarayya da hukumar FCT da su gudanar da cikakken bincike kan halin da cibiyoyin lafiya ke ciki a Abuja, domin gano sassan da ke bukatar fadadawa, gyarawa da kuma karin kayan aiki.

A ƙarshe, majalisar wakilai ta yanke shawarar kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da cikakken bincike kan tsarin lafiyar Abuja tare da mikawa majalisa rahoto da shawarwari cikin mako huɗu.

Tinubu ya dauki matakin karya farashin magunguna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa MediPool, wata ƙungiyar haɗin gwiwar sayayya ta ƙasa, domin rage farashin kayayyakin kiwon lafiya.

Ministan lafiya, Ali Pate, ya bayyana cewa za a gudanar da MediPool ne bisa haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni domin samar da magunguna masu rahusa.

Ayyukan ƙungiyar za su haɗa da tsara saye da rarraba kayan kiwon lafiya, da kuma tallafa wa masana’antun cikin gida domin ƙarfafa samar da magani a farashi mai sauki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.