'MediPool': Matakin da Tinubu Ya Dauka don Karya Farashin Magunguna a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa MediPool, ƙungiyar sayayya ta ƙasa, don rage farashin kayayyakin kiwon lafiya a Najeriya
- Ministan lafiya, Ali Pate ya ce MediPool za ta samar da magunguna masu rahusa ta hanyar haɗin gwiwa da gwamnati da kuma kamfanoni
- Ayyukan su sun haɗa da tsara sayayya, rarrabawa da kula da kayayyaki, tabbatar da inganci, da tallafa wa masana'antun cikin gida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ya amince da kafa MediPool, wata ƙungiyar sayayya ta kasa.
Majalisar FEC ta amince da kafa kungiyar MediPool a matsayin wani gagarumin mataki da zai taimaka wajen rage farashin kayayyakin kiwon lafiya.

Asali: Twitter
Ministan lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan fitowa daga taron a Abuja, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati za ta karya farashin magunguna
Farfesa Ali Pate ya bayyana cewa Medipool, za ta zama mai samar da muhimman magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a faɗin Najeriya, a farashi mai rahusa.
Ya ce MediPool za ta yi aiki a matsayin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, ta hanyar amfani da ƙarfin sayayyar gwamnatin tarayya don saukar da farashi.
Ya ƙara da cewa za a kafa ta ne ta hanyar asusun tallafin kiwon lafiya na gwamnatin tarayya sannan daga ƙarshe a fadada ta zuwa manyan asibitocin gwamnati.
Ministan lafiyar ya ce:
"Wannan tsarin zai inganta samar da kulawar kiwon lafiya, samar da kuɗaɗe, ta yadda a matsayinmu na masu saye, za mu iya tattaunawa kan farashin kayan.
"Wannan tsarin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin tarayya na rage tsadar kiwon lafiya, ta hanyar sake fasalin kasuwar cikin gida da samar da sauƙin samun ingantattun magunguna."
Maunufar samar da kungiyar MediPool
Ali Pate, wanda ya lura cewa 'yan Najeriya sun fuskanci wahalhalu kwanan nan wajen samun ingantattun magunguna, ya ce an kafa MediPool ta yadda za a iya samun magunguna a farashi mai rahusa.
A cewarsa:
"Manufar shugaban kasa ga 'yan Najeriya ita ce su sami magunguna masu rahusa da kuma sauƙaƙa masu samun ingantattun magunguna.
"Wannan shi ne aikin da muka shafe watanni da yawa muna yi. A gaskiya ma, kusan shekara ɗaya da rabi, gwamnati na ƙoƙarin nemo hanyoyi daban-daban don rage farashi, saboda mun san cewa 'yan Najeriya na fama da hauhawar farashin magunguna."

Asali: Twitter
Ayyukan da MediPool za ta yi
Jaridar The Cable ta ruwaito ministan ya bayyana cewa ayyukan MediPool sun hada da:
"Tsara sayayya, saka idanu kan rarraba magunguna, samar da magunguna, kula da magunguna, tabbatar da inganci, bin ƙa'idoji, da kuma tabbatar da cewa an tallafa wa masana'antun cikin gida.
"Ya kuma ƙunshi maye gurbin shigo da magunguna, kula da kuɗi da tsarin biya, gina ƙarfin aiki da horo, da kuma tsara yadda za a magance matsaloli don tabbatar da samuwar magunguna ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni."
Ya ce an tantance Medipool ta hanyar hukumar kula da haɗin gwiwar kayayyakin more rayuwa kuma an kwatanta ta da wasu manyan ƙungiyoyin sayayya na duniya a Kenya, Afirka ta Kudu, Singapore, Saudi Arabia, da wasu ƙasashe da yawa.
Shirin gwamnati na sayen magunguna
Tun da fari, mun ruwaito cewa a watan Disambar 2024, gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta na sayen magunguna domin magance karuwar farashin magani.
Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate ya ce wannan matakin zai taimaka wajen rage radadin farashin kayan kiwon lafiya ga al’umma da kuma inganta lafiyar jama’a.
Hakazalika, Farfesa Pate ya ce gwamnatin tarayya na da burin inganta samar da inshorar lafiya ga marasa galihu da kuma kara yawan magunguna da kayan aikin asibiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng