An Fara Raba Tallafin Gwamnatin Tinubu, Mutane Miliyan 15 Za Su Ci Gajiyar Shirin

An Fara Raba Tallafin Gwamnatin Tinubu, Mutane Miliyan 15 Za Su Ci Gajiyar Shirin

  • Gwamnatin tarayya ta ba mutane miliyan shida tallafin kudi cikin wata shida da suka gabata a Najeriya domin rage matsi da kuncin tattali
  • Ministan jin kai ya ce an cire bayanan karya daga rajistar tallafi, an kuma fara amfani da fasahar zamani don tabbatar da cancanta da gaskiya
  • Ya bayyana cewa shugaban kasa ya umurci a bai wa gidaje miliyan 15 tallafin kudi kafin watan Oktoba, tare da hadin gwiwa da Bankin Duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan harkokin jin kai da walwala, Farfesa Nentawe Yilwatda ya fadi yawan mutane da suka samu tallafi.

Yilwatda ya bayyana cewa mutane miliyan shida ne suka ci gajiyar shirin tallafin kudi na gwamnatin tarayya cikin wata shida.

Matasa miliyan 15 za su ci gajiyar tallafi
Gwamnatin Tinubu za ta raba tallafi ga matasa miliyan 15. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Asali: Facebook

Miliyoyin mutane da suka ci gajiyar shirin

Yilwatda ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga masu amfana da shirin horo na Skills-to-Wealth (S2W) a Jos, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce a baya, mutane miliyan biyu ne kawai suka ci gajiyar shirin a cikin shekaru tara da suka gabata, amma yanzu an canza salo.

Ya ce:

“Muna yin rajistar zamani na duka gidaje a cikin kundin bayanai, muna ba su katin shaidar zamani da asusun e-wallet, sannan muna tantancewa da hannu.
“Muna cire duk wasu bayanan karya daga kundin rajista wadanda ba mu iya tabbatarwa ko ganewa ba.
“A cikin watanni shida kacal, mun kai tallafi ga mutane miliyan shida, wato matsakaicin mutane miliyan daya a kowane wata.

Ministan ya kara da cewa ana sa ran mutane miliyan 15 za su shiga shirin nan da watan Oktoba.

“Shugaban kasa na da niyyar tallafa wa gidaje miliyan 15 kafin watan Oktoba, ya bayar da umarni cewa a raba kudin ga masu amfana cikin wata tara."

- Cewar Yilwatda

Za a raba tallafi ga matasa
Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da raba tallafi. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Asali: Twitter

Yadda aka raba tallafin ga mutane

Yilwitda ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta hada kai da Bankin Duniya don tabbatar da ingancin jerin sunayen masu amfana, cewar The Nation.

Ya kara da cewa:

“Bayan raba kudin ga mutane miliyan hudu na farko, na bukaci Bankin Duniya ta tura wata tawaga mai zaman kanta domin tabbatar da sunayen.
“Muna so mu tabbatar da ingancin abin da muke yi, kuma sakamakon ya nuna cewa wadanda aka biya suna cikin kundin rajista.
“Tawagar tantancewa ta ziyarci gidajen wadanda suka ci gajiyar shirin, inda suka gana da kashi 96 cikin 100 daga cikinsu.
“Sauran kashi hudu da ba a gan su ba na zaune ne a wuraren da ba a iya zuwa ko kuma sun bar yankinsu saboda matsalar tsaro."

Game da shirin Skills-to-Wealth, ministan ya bayyana cewa an kirkire shi ne domin bai wa matasan Najeriya horo a fannoni uku: noma, makamashi, da motoci.

Tinubu zai tallafa wa matasa miliyan 5

Kun ji cewa gwamnatin tarayya na shirin tallafa wa mata miliyan 4.5 a fadin Najeriya a karkashin wani shiri da za a yi hadaka da bankin duniya.

Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bukaci daukar mataki cikin gaggawa don aiwatar da shirin ba tare da bata lokaci ba.

Majiyoyi sun ce bankin Duniya ya amince da bayar da tallafin Dala miliyan 500 domin aiwatar da shirin a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.