A Karshe, An Fara Duba Marasa Lafiya a Babban Asibitin da Buhari Ya Kafa a Arewa
- Asibitin ƙashi na ƙasa da ke Jos zai fara aiki bayan shekaru huɗu da kafuwa, inda za a fara duba marasa lafiya daga ranar Talata
- Shugaban asibitin ya ce asibitin na ɗaya daga cikin asibitoci uku da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kafa a shiyyoyi uku
- An rahoto cewa asibitin zai kula da masu matsalar ƙashi ne kawai, ba zai kula da masu ciki ko cutar zazzabin cizon sauro da sauransu ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato: Asibitin ƙashi na ƙasa da ke Jos, jihar Filato, ya fara aiki bayan shekaru huɗu da kafuwa, inda masu matsalar kashi ke samun kulawa ta musamman.
Shugaban asibitin, Farfesa Icha Onche, ya bayyana haka a ranar Litinin, 12 ga Mayu, a wani taron manema labarai da ya kira a Jos.

Asali: Twitter
Asibitin kashi da Buhari ya kafa a Jos zai fara aiki
A matsayin wani ɓangare na fara ayyukan asibitin a hukumance, Farfesa Onche ya ce asibitin zai fara karɓar marasa lafiya daga ranar Talata, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce asibitin ƙashi na ƙasa da ke Jos, yana ɗaya daga cikin asibitoci uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa su a kwanakin ƙarshe na mulkinsa.
Ya bayyana cewa akwai irin waɗannan asibitoci a Benin da Jalingo, waɗanda aka kafa don tabbatar da daidaiton yanki, musamman a yankunan da ba su da irin waɗannan cibiyoyin kiwon lafiya na musamman.
Ayyukan da asibitin kashin zai rika yi
Farfesa Onche ya bayyana cewa asibitin ƙashi ne kawai, inda za a rika kula da masu lalurar ƙasusuwa, tsokoki, jijiyoyi da sauran abubuwan da suka shafi motsin jiki.
Ya yi bayanin cewa ba su da kayan aiki kuma ba huruminsu ba ne duba mata masu ciki, masu zazzabin cizon sauro, tarin fuka, gudawa, hawan jini, ciwon sukari, ko tari.
Ya shawarci mutane da su je cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, ko manyan asibitoci, ko manyan cibiyoyin kiwon lafiya kamar JUTH don irin waɗannan matsalolin.

Asali: Facebook
Asibitin na bukatar karin kudi daga gwamnati
Jaridar Independent ta ruwaito cewa asibitin, wanda Buhari ya kafa a 2021 kuma yake da matsugunnin a ginin tsohon asibitin koyarwa na jami'ar Jos, ya sha gyare-gyare sosai don zama cikakkiyar cibiyar kiwon lafiya.
Farfesa Onche ya tabbatar da cewa asibitin yana da ƙarfin yin manyan aiyuka, gami da sauya haɗin gwiwar cinya da idan sahu, kuma za su yi ƙoƙari su rage buƙatar 'yan Najeriya ta zuwa ƙasashen waje.
Farfesan ya bayyana cewa kasafin kuɗin da aka warewa asibitin a 2025 bai haura Naira miliyan 600 ba, wanda ba zai iya isa a biya buƙatun asibitin ba.
Rigima ta kaura a JUTH kan sanya hijabi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gumurzu ya ɓarke a asibitin koyarwa na jami'ar Jos saboda zargin tilasta wa ɗalibai mata Musulmai cire hijabi a sashin kiwon lafiya na asibitin.
Daliban sun fusata, inda suka zargi shugaban sashin da cin zarafin su, har ma da ba su zaɓin barin makaranta ko barin gashin kansu a buɗe.
Matakin shugaban sashen ya ci karo da dokar ƙungiyar ma'aikatan jinya ta ƙasa da ke ba ɗalibai musulmi da kirista damar sanya mayafi saboda addininsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng