Ta Faru Ta Kare: Majalisar Dattawa Ta Amince da Kudurorin Gyaran Haraji na Tinubu

Ta Faru Ta Kare: Majalisar Dattawa Ta Amince da Kudurorin Gyaran Haraji na Tinubu

  • Majalisar dattawa ta amince da dokokin gyaran haraji biyu daga cikin huɗu da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata
  • 'Yan majalisar sun amince da kudurorin ta hanyar kada kuri'ar murya bayan rahoton kwamitin da aka kafa don duba dokokin
  • Shugaban sanatocin ya ce majalisar za ta amince da sauran dokokin biyu da suka hada da dokar haraji ta Najeriya ta 2024 a ranar Alhamis

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar Dattawa ta amince da biyu daga cikin kudurorin dokar gyaran haraji huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

Dokokin biyu da aka amince da su sune: Dokar kafa hukumar haraji ta Najeriya da dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji.

Majalisar dattawa ta amince da kudurorin dokokin haraji 2 cikin 4 da Tinubu ya gabatar mata
Shugaba Bola Tinubu yayin da ya ke jawabi a gaban majalisar tarayya. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Majalisa ta amince da kudurorin gyaran haraji

An amince da waɗannan dokokin ne bayan da sanatoci suka duba rahoton kwamitin wucin gadi wanda Sanata Sani Musa daga Niger ta Gabas ya jagoranta, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kafa kwamitin ne domin magance cece-kuce da sabanin da aka samu game da wasu bangarori da ke cikin kudurorin gyaran harajin.

A ranar Laraba, sanatocin sun tattauna kuma sun yi la'akari da kowane sashe na dokokin a karkashin kwamitin majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da amincewa da kudurorin bayan da mafi yawan sanatoci suka goyi bayansu ta hanyar zaɓen murya.

An sanya ranar amincewa da sauran kudurorin

Mista Akpabio ya ce majalisar dattawa za ta kafa kwamiti don daidaita matsayarta kan dokokin, kamar yadda majalisar wakilai ta yarda da su a watan Maris.

Shugaban majalisar ya shaida cewa da zarar an kammala daidaitawar, za a miƙa dokokin da aka amince da su zuwa ga Shugaba Tinubu don amincewa da su.

Majalisar dattawa ta amince da kudurorin gyaran haraji da Tinubu ya gabatar
Zauren majalisar dattawa, Abuja. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

An rahoto cewa idan shugaban kasar ya amince da wadannan kudurori, kuma ya rattaba hannu kansu, to daga nan sun zama doka.

Sanata Akpabio ya ce majalisar za ta amince da sauran dokoki biyu: Dokar haraji ta Najeriya ta 2024 da dokar gudanar da haraji, a ranar Alhamis.

Majalisar wakilai ta amince da kudurorin haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar Wakilai ta amince da kudirorin gyaran haraji bayan nazari daga kwamitin bai daya, ƙarƙashin jagorancin Abbas Tajudeen.

Daya daga cikin manyan batutuwa da aka amince da su shi ne tsarin rabon VAT da kuma kin amincewa da karin VAT din zuwa kashi 10%.

Sai dai, duk da amincewar majalisar wakilan, har yanzu kudurorin ba su zama doka ba, ana jiran amincewar majalisar dattawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.