Tinubu Ya Dakatar da Fubara: Yadda Shugaban Ƙasa Ke Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Jihohi
- Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa a ranar Talata
- Kundin tsarin mulkin Najeriya, sashe na 305, ya bai wa shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta ɓaci idan akwai matsalar tsaro ko rikicin siyasa a jiha
- Shin wannan mataki da Tinubu ya dauka yana bisa doka? Kuma ta yaya ake ayyana dokar ta ɓaci a Najeriya? Legit Hausa ta yi cikakken bayani a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.
Wannan mataki na zuwa ne bayan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar, wanda ya hada da sabani tsakanin gwamnan da wasu bangarorin majalisar dokokin jihar.

Asali: Facebook
Bayan dakatarwar, shugaba Tinubu ya nada shugaban rikon kwarya domin tafiyar da harkokin jihar har na tsawon wanni shida, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin wannan mataki da Tinubu ya dauka yana bisa doka? Kuma ta yaya ake ayyana dokar ta ɓaci a Najeriya?
Mece ce Dokar Ta Ɓaci?
Dokar ta ɓaci wata doka ce da ake ayyanawa a wata jiha ko ƙasa gaba ɗaya idan an samu gagarumin rikici da ya fi ƙarfin hukumomin jiha su shawo kansa.
A irin wannan yanayi, shugaban ƙasa na iya ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da doka da oda, wanda ka iya haɗawa da dakatar da gwamna da majalisar jiha, tare da nada shugaban rikon kwarya.
A Najeriya, sashe na 305(1)–(6) na kundin tsarin mulki na 1999 ya ba wa shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta ɓaci a kowane yanki na ƙasar, amma sai bayan ya samu amincewar majalisar dokoki ta kasa.
Matakan ayyana dokar ta ɓaci a Najeriya
A bisa doka, rahoton Vanguard ya nuna cewa shugaban ƙasa na bin wasu matakai kafin ayyana dokar ta ɓaci kamar haka:
1. Dalilin ayyanawa
- Rikicin tsaro da ya gagari gwamnati.
- Rashin zaman lafiya da ya kai matakin barazana ga ƙasa.
- Rikicin siyasa da ke iya haddasa rugujewar gwamnatin jiha.
2. Tuntubar majalisar tarayya
Dole ne shugaban ƙasa yana da bukatar samun amincewar majalisar tarayya kafin aiwatar da dokar ta ɓaci.
3. Ayyanawa da aiwatarwa
- Idan majalisar tarayya ta amince, shugaban ƙasa zai fitar da sanarwa ta musamman, inda za a ayyana dokar ta baci a jihar.
- Shugaban kasa na iya dakatar da gwamna da majalisar jiha idan lamarin ya bukaci hakan.
- Hakazalika, shugaban kasa zai iya girke sojoji ko ƙara ƙarfin jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a jihar.
4. Nada shugaban rikon kwarya
- Idan an dakatar da gwamna yayin ayyana dokar ta-bacin, shugaban ƙasa na da ikon nada wani sabon shugaban rikon kwarya.
- Wannan na zuwa ne bisa shawarar gwamnatin tarayya.
5. Sake duba matsalar bayan wani lokaci
- Dokar ta ɓaci na iya ɗaukar watanni shida, amma za a iya tsawaita ta idan an ga bukatar yin hakan.
- Idan an shawo kan matsalar, za a dawo da tsarin dimokuraɗiyya a jihar da abin ya shafa.
Shugabannin da suka ayyana dokar ta-zcbaci a Najeriya

Asali: UGC
1. Olusegun Obasanjo
A 2004, tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Plateau saboda rikicin kabilanci da addini da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya dakatar da gwamnan jihar, Joshua Dariye, tare da nada tsohon babban hafsan soji, Janar Chris Alli, a matsayin shugaban rikon kwarya, inji rahoton VOA.
A 2006, ya kuma ayyana dokar ta ɓaci a Ekiti saboda rikicin siyasa tsakanin Gwamna Ayo Fayose da majalisar dokoki ta jihar.
2. Goodluck Jonathan
A Mayun 2013, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa saboda hare-haren Boko Haram da suka yi kamari a yankin Arewa maso Gabas.
Bayan ayyana dokar, gwamnatin tarayya ta ƙarfafa matakan tsaro a yankin, tare da girke sojoji da sauran jami’an tsaro.
APC ta nemi Tinubu ya ayyana dokar ta baci
Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta ɓaci a Rivers saboda rikicin siyasa da ya ɓarke.
Jam’iyyar ta yi gargadin cewa, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, rikicin na iya rikidewa zuwa barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng