Gwamna Ya Yi Magana da Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Mutu a Hannun Ƴan Bindiga
- Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya yi magana bayan mutuwar tsohon ɗan majalisa a hannun ƴan bindiga
- Namadi ya bayyana alhini kan rasuwar Abba Anas Adamu, yana cewa babban rashi ne ga Jigawa da Najeriya
- Rahotanni sun ce masu garkuwa sun kashe marigayin bayan sun karɓi kuɗin fansa daga iyalansa, sannan suka jefar da gawarsa a wani fili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar tsohon ɗan majalisar wakilai.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Hon. Abba Anas Adamu ya rasa ransa ne a hannun ƴan bindiga duk da biyan makudan kudin fansa.

Source: Facebook
Gwamna Namadi ya bayyana alhininsa ne jim kaɗan bayan halartar sallar jana’izar marigayin da aka yi a Kano, cewar Premium Times.
Yaushe aka yi sallar jana'izar marigayin?
An gudanar da sallar jana'izar marigayin a yau Talata 12 ga watan Mayun shekarar 2026 da muke ciki tare da iyalai da abokan siyasa.
Gwamnan ya bayyana cewa rasuwar Hon. Abba Anas babban rashi ne ga Jigawa da Najeriya baki ɗaya.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan masu garkuwa da mutane sun kashe shi, duk da sun karɓi kuɗin fansa daga iyalansa, sannan suka jefar da gawarsa a wani fili.
Gwamna Namadi ya halarci sallar jana'izar marigayin
A wajen jana’izar, gwamnan ya haɗu da abokai, ’yan uwa da masu jimami wajen gudanar da addu’o’i domin neman rahama da gafara ga marigayin.
Gwamnan ya bayyana marigayi Abba Anas Adamu a matsayin jajirtaccen bawan jama’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima da cigaban jama’a.
Ya ce marigayin ya riƙe muƙamai daban-daban a harkokin gwamnati, ciki har da tsohon ɗan majalisar wakilai, shugaban ƙaramar hukumar Guri da kwamishina a Jigawa.

Source: Facebook
Gudunmawar da marigayin dan siyasar ya bayar
Haka kuma, gwamnan ya ce marigayin ƙwararren malami ne wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasa siyasa da dimokuraɗiyya a Jigawa da Najeriya.
Gwamna Namadi ya ce za a tuna da marigayin saboda tawali’unsa, jajircewa kan tsarin dimokuraɗiyya da kuma irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban siyasar Jigawa.
A ƙarshe, gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin kura-kuransa tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdaus mai daraja, cewar PM News.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya bai wa iyalansa, abokansa, abokan siyasarsa da daukacin al’ummar Jigawa juriyar ɗaukar wannan babban rashi mai raɗaɗi.
Yan bindiga sun harbi tsohon kwamishinan Zamfara
An ji cewa wani tsohon kwamishina a Zamfara ya tsallake rijiya ta baya bayan wani mummunan harin ƴan bindiga.
An ce Sheikh Abdullahi Maharazu Mafara ya gamu da tsautsayi bayan ‘yan bindiga sun bude masa wuta a hanyar zuwa taron siyasa
Lamarin ya faru ne yayin da yake tafiya daga Talata Mafara zuwa Gusau domin halartar taron APC, inda aka yi masa kwanton bauna tare da harbe-harbe.
Asali: Legit.ng

