Yan Najeriya Sun Taso Bankin Duniya a Gaba kan ba Tinubu Bashin $1.25bn
- ’Yan Najeriya sun cika shafukan Bankin Duniya da martani mai zafi kan shirin ba gwamnatin Bola Tinubu sabon bashin dala biliyan 1.2
- Bankin Duniya ya ce ya takaita sashen sharhi a wasu bangarorin shafinsa na Instagram bayan yawaitar martani daga ’yan Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa idan aka amince da bashin, jimillar kudaden da Bankin Duniya ya bai wa Najeriya za su kai kusan dala biliyan 10
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yan Najeriya sun dura kan Bankin Duniya game da shirin ba shugaban Najeriya, Bola Tinubu bashin $1.25bn.
Bayan caccakarsa da yan Najeriya suka yi, bankin ya bayyana cewa ya takaita sharhi a wasu sassan shafinsa na Instagram bayan martani daga ’yan kasar.

Source: Twitter
An caccaki Bankin Duniya kan bashin Tinubu
Martanin ya biyo bayan rahoton musamman na jaridar The Punch gwamnati na tattaunawa da Bankin Duniya domin sabon lamuni.
An shirya gabatar da bashin mai suna “Nigeria Actions for Investment and Jobs Acceleration” domin amincewa a ranar 26 ga Yuni, 2026, kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Idan aka amince, bashin zai zama na biyu mafi girma da Bankin Duniya ya taɓa bai wa Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
A canjin N1,361.4 kan dala ɗaya, wannan bashin zai kai kusan tiriliyan N1.70, wanda ke nuna girman bashin da ake ci gaba da nema.
Abin da yan Najeriya ke bukata
’Yan Najeriya sun cika shafukan Bankin Duniya da kira a dakatar da ƙarin lamuni, suna nuna damuwa kan bashi da matsin tattalin arziki.
Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin masu hulɗa da shafin Instagram ɗin Bankin Duniya saboda tattaunawa kan wannan sabon bashi.
Sai dai bincike ya nuna cewa matsalar takaita sharhin na iya zama ta na’ura ce kawai, ba wai martanin jama’a kai tsaye ba.
Wata majiya ta Bankin Duniya ta ce wannan batu na iya zama matsalar fasaha, ba wani abu da ya shafi korafe-korafen ’yan Najeriya ba.

Source: Twitter
Tulin basuka da Bankin Duniya ya ba Najeriya
Bankin Duniya ya riga ya amince da sama da dala biliyan 9.35 ga Najeriya tsakanin 2023 zuwa 2026 a fannoni daban-daban, cewar Arise TV.
Idan aka ƙara wannan sabon bashin, jimillar bashin da aka amince zai kai kusan dala biliyan 10.6 a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Duk da haka, yawancin bashin ba a fitar da shi kai tsaye ba, sai an cika sharuddan gyare-gyare kafin a saki kuɗaɗen.
Najeriya za ta kashe $11bn kan biyan bashi
A wani labarin, an ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce kusan rabin kudaden shiga na Najeriya a 2026 za su tafi ne wajen biyan basussukan da ake bin kasar.
Ya koka kan yadda tsarin hada-hadar kudin duniya ke hana kasashen Afirka samun rancen da ya dace domin bunkasa masana’antun su.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron 'Africa Forward Summit' da aka gudanar a Nairobi, kasar Kenya.
Asali: Legit.ng

