Albishir: Najeriya Za Ta Kaddamar da Sabon Tsarin Watsa Shirye Shiryen Talabijin

Albishir: Najeriya Za Ta Kaddamar da Sabon Tsarin Watsa Shirye Shiryen Talabijin

  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Najeriya ta kammala shirye-shiryen fara tsarin talabijin na zamani
  • Sabon tsarin zai samar da tashoshin talabijin sama da 100 tare da inganta daukar hoto daga SD zuwa HD a Najeriya
  • Gwamnati ta ce tsarin zai kara gasa, bunkasa harkar talla da samar da ingantaccen kallon talabijin ga ‘yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Najeriya ta kammala dukkan shirye-shiryen fara aiwatar da tsarin watsa shirye shiryen talabijin na zamani (DSO) a fadin kasa. Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai hukumar NIGCOMSAT da ke cikin Obasanjo Space ranar Laraba, 13 ga Mayun 2026.

Najeriya za ta koma tsarin zamani a shirye shiryen talabijin
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris na jawabi ga ƴan jarida a Abuja. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Sabon tsarin talabijin a Najeriya

Mohammed Idris ya kai wannan ziyarar ne tare da da shugaban hukumar NBC, Charles Ebuebu, da shugabar NIGCOMSAT, Jane Egerton-Idehen, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Kasar Saudiyya ta yi gyare gyare, ta tura tallafi ga kasashen Musulmi 27

Ministan watsa labaran ya ce tsarin zai fara aiki a hukumance a ranar 17 ga Yunin 2026, yana mai cewa:

“Wannan sabon tsari ne na zamani, mun shiga namu zamanin.”

Mohammed Idris ya bayyana sabon tsarin a matsayin babban ci gaba ga bangaren yada labarai a Najeriya.

A cewarsa:

“Wannan sabon zamani ne ga kasarmu. Bangaren yaɗa labarai ya fara ganin cikar alkawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na gyaran fannoni daban-daban."

Ya kara da cewa bayan shekaru masu yawa na jinkiri, Najeriya na dab da kammala sauya tsarin 'analog' zuwa tsarin zamani.

Fa’idodin sabon tsarin talabijin

A cewarsa, tsarin zai taimaka wajen gano yawan masu kallon tashoshi da irin shirye-shiryen da suke kallo.

“Za a san wanda ke kallon tashar talabijin, abin da yake kallo da kuma yawan mutanen da suke kallo.”

Ya ce hakan zai taimaka wa masu talla da gidajen yada labarai wajen tsara shirye-shiryensu cikin sauki.

Za a samu tashoshi sama da 100

Shugaban Hukumar NBC, Charles Ebuebu, ya ce za a fara da tashoshi sama da 100 a ranar da za a kaddamar da tsarin.

Kara karanta wannan

Kawancen PDP da APM: Gwamna Makinde zai ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2027

Ya ce sabon tsarin ya dace da sababbin fasahohi da yadda mutane ke kallon talabijin a zamanance, in ji rahoton Punch.

Ya kara da cewa an samar da cibiyoyin gudanar da shirye-shiryen da kuma wuraren kula da kwastomomi a yankuna daban-daban na kasar.

Za a ƙaddamar da sabon tsarin talabijin na zamani a Najeriya
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya na duba dakin shirye shiryen talabijin na cibiyar NIGCOMSAT. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Talabijin zai koma HD

Tun da fari,.Mohammed Idris ya ce wannan sabon tsarin zai karya tsarin mamaya da wasu tsirarun kamfanoni suka yi a bangaren talabijin.

Ya ce yanzu za a samu gasa mai kyau tsakanin gidajen talabijin, sannan Najeriya za ta koma daga tsarin SD zuwa HD.

Hakan na nufin masu kallo za su rika samun ingantaccen hoto da sauti ta hanyar tauraron dan adam da manhajojin waya.

Minista ya gwarzanta gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya kwararo yabo ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu

Alhaji Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa waɗanda suka gabace ta nisa nesa ba kusa ba.

Ministan ya nuna cewa gwamnatin ta samu nasarori waɗanda gwamnatocin baya ba su same su ba a cikin shekara biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com