Sarkin Zazzau Ya Fadi Dalilin Tilastawa Fadawansa Komawa Islamiyya
- Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya umarci fadawansa da su koma makarantar Islamiyya don su gyara addininsu
- Ya bayyana cewa wannan yana daga cikin matakin sauke nauyin da Allah Subhanahu wa Ta'ala ya dora masa na jama'arsa
- Ahmad Nuhu Bamalli ya ce ya samo wannan tsari ne daga mahaifinsa, wanda shi ma ya tilastawa fadawansa komawa karatun Islamiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya umarci fadawansa da su koma makarantar Islamiyya domin gyara kuskuren da ake tafkawa a addini.
Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa yana daga cikin hakkinsa a matsayinsa na jagora ya tabbatar da cewa an gyara yadda jama’a ke tafiyar da addininsu.

Asali: Facebook
A wata hira ta musamman da RFI Hausa, Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan yadda dattawa ke yin kuskure wajen yin alwala, balle tayar da iqamar sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Mayar da Fadawan Sarkin Zazzau Islamiyya
Ahmad Nuhu Bamalli ya ce ya dauko wannan tsari ne kamar yadda ya ga mahaifinsa ya yi a baya — wajen dagewa domin ganin jama’a sun san addini kamar yadda Allah Subhanahu wa Ta’ala ya umarta.
Ya bayyana cewa:
“Mutum bai iya alwala ba, bai iya wankan janaba ba, ta yaya zai yi sallah? Kuma Allah Ya ce kada ka bauta Masa sai ka san Shi. To, baka san Shi ba, ba ka bi hanyar da za ka san Shi ba.”
Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana yadda mahaifinsa ya tilasta wa fadawansa komawa Islamiyya domin inganta addininsu.
Ya ce:
“A masallaci za mu yi sallar Asuba, liman bai zo ba, sai ya ja sallah. Sai ya waigo ya ga yadda muka tsaya, ya juya don a ta da iqamar sallah, a gurin ikama ya gagara.”
Sarkin ya shawarci sauran masarautun kasar nan da su dauki irin wannan hanya ta inganta addinin mabiyansu don su kubuta ranar gobe.
Sarkin Zazzau ya ankarar da Shugabanni
Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana cewa ya kamata shugabanni su tsaya wajen tabbatar da sauke nauyin da Allah ya dora musu kafin su hadu da Shi a ranar Alƙiyama.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Al-Qur’ani na dauka, na rantse, na ce zan yi kaza, zan yi kaza, zan hana kaza a gaban mutane fiye da miliyan. To wannan misali ka yi kira, a kana bin abin da Allah Ya ce. Idan bai yi ba, na sauke nauyi na ko ban sauke ba?”
Ya nanata cewa dukkanin shugabanci ba wasa ba ne a ranar Alƙiyama. Saboda haka duk shugaban da ke son ya ji sauƙi, sai ya tabbata ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Basarake ya yi murabus a Zazzau
A baya, mun ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, ya tabbatar da nada Alhaji Shehu Abdullahi a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.
Alhaji Shehu Abdullahi, wanda ke da shekara 61, tsohon jami’i ne a hukumar daidaita farashin man fetur na kasa (NMDPRA) da ke Abuja, ya rike matsayin babban jami’in kudi.
Alhaji Shehu Abdullahi ƙani ne ga Farfesa Ango Abdullahi, wanda ya rike sarautar Magajin Rafi tsawon lokaci kafin ya ajiye mukamin saboda shekaru da kuma yanayin lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng