Hadakar Adawa: Babachir Lawal Ya Fadi Matsayar PDP a Shirin Kifar da Tinubu
- Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana cewa kawancen siyasa da suke kokarin ginawa ba ta da niyyar aiki da PDP
- Ya tabbatar da cewa Atiku Abubakar na taka muhimmiyar rawa a sabon yunkurin kafa jam’iyya da hadaka mai karfi gabanin 2027
- A cewarsa, gwamnatin Bola Tinubu tana nuna wariya da tsana ga marasa galihu, wanda ya sabawa akidar CPC da aka samar bisa kare hakkokin talaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir David Lawal, ya bayyana cewa kawancen jam'iyyunsu ba zai yi amfani da PDP a shirinsu na 2027 ba.
Babachir Lawal ya bayyana cewa PDP ba ta da wani amfani a hadin gwiwar siyasa da ake kokarin ginawa, inda ya bayyana jam’iyyar da kwayar cuta da ba za a iya warkar da ita ba.

Asali: Facebook
A wata hira da aka yi da shi a Jaridar Punch, tsohon Sakataren gwamnati a lokacin Muhammadu Buhari ya kara da cewa a duk zaman da suke yi, babu inda aka nuna goyon bayan amfani da PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babachir ya fadi girman Atiku a PDP
Babachir ya tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yana taka rawar gani a shirin kafa sabuwar jam’iyya.
Ya ce:
"A duk zaman da na halarta don tattaunawa kan hadakar siyasa, ba a taba kawo sunan PDP ba. Mutane da dama sun fada mana PDP ba za ta iya gyaruwa ba.”
“Atiku yana da kishin hadin kan ’yan adawa fiye da kowa. Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne a samu sabuwar jam’iyya, a ci gaba da tafiya da tsarin dimokuradiyya har sai an kai ga taron kasa da za a fitar da ’yan takara."

Asali: Twitter
Ya ce akwai yiwuwar Atiku zai fice daga PDP idan ya shiga sabuwar jam’iyyar da ake shirin kafa wa, saboda “ba za ka iya zama a jam’iyya biyu ba lokaci guda.”
Babachir: 'Tinubu na kuntatawa Talaka'
Injiniya Babachir Lawal ya zargi gwamnatin Tinubu da wulakanta marasa galihu da kuma kawo wahala ga ’yan Najeriya.
Ya ce:
“Gwamnatin nan tana da wata dabi’a mai kama da tsanar talaka. A ganinsu, ganin talaka ma yana bata musu rai. Wannan ya saba da abin da CPC ta tsaya a kai, wanda shi ne nganta rayuwar talakawa da yakar zalunci.”
Ya bayyana cewa ‘yan asalin CPC, jam’iyyar da suka kafa tare da Buhari kafin hadewar da ya haifar da APC, na shirin kafa sabuwar jam'iyya don kalubalantar Bola Tinubu.
'Za mu fatattaki Tinubu,' Babachir Lawal
A baya, mun wallafa cewa Babachir Lawal, ya bayyana matuƙar damuwa da halin da Najeriya ke ciki a ƙarƙashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana mai dole a yi fafutukar canji.
Tsohon sakataren gwamnatin ya kara da sukar gwamnatin Tinubu bisa yadda take tafiyar da al’amura, yana zargin cewa gwamnatin tana nuna wariya a tsakanin 'yan Najeriya.
Babachir ya bayyana cewa waɗanda ke neman samun goyon bayan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, daga ciki har da masu mara wa Tinubu baya na bata lokacinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng