Tsugune ba Ta Ƙare ba: An Sauya Alkalin da Zai Jagoranci Shari'ar ADC da Tsagin Nafiu Bala

Tsugune ba Ta Ƙare ba: An Sauya Alkalin da Zai Jagoranci Shari'ar ADC da Tsagin Nafiu Bala

  • Babban Alkalin Kotun Tarayya ta sauya alkalin da ke jagorantar shari'ar rikicin shugabanci a jam'iyyar ADC mai adawa
  • Kotun ta mayar da karar da Nafiu Bala ya shigar kan shugabancin ADC zuwa wani sabon alkali domin ci gaba da sauraron shari'ar
  • Nafiu Bala na neman hana David Mark da Rauf Aregbesola tare da kwamitin rikon kwarya gudanar da ayyukan shugabancin jam'iyyar ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsugune ba ta ƙare ba game da rikicin jam'iyyar ADC wanda shugaban tsaginta, Nafiu Bala ya shigar da kara.

An mayar da karar da ke kalubalantar shugabancin jam'iyyar ADC zuwa hannun wani sabon alkali a Babbar Kotun Tarayya.

An sauya alkalin da ke jagorantar shari'ar ADC da Nafiu Bala
Shugaban ADC, David Mark, Nafiu Bala da Atiku Abubakar. Hoto: ADC Vanguard.
Source: Twitter

Babban Alkalin Kotun Tarayya ne ya sauya shari'ar daga hannun alkali mai shari'ar a baya zuwa wani alkali domin yanke hukunci, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Adamawa: Sarkin Mota ya samu takara a NDC, za a fafata da shi a zaben 2027

Dalilin Nafiu na shigar da tsagin Mark kara

An ba Alkali Peter Lifu damar sauraron karar bayan tsohon alkalin, Emeka Nwite, ya samu shawarar daukaka zuwa Kotun Daukaka Kara.

Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, shi ne ya shigar da karar kalubalantar sabon shugabancin ADC.

Yana neman hana David Mark, sakataren kasa Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya ci gaba da jagoranci.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, Bala ya ce tsarin da aka bi wajen kafa shugabancin rikon kwarya ya saba doka.

Ya yi zargin cewa tsarin ya karya tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyyar ADC da kuma Dokar Zabe ta kasa.

Wadanda aka shigar da kara sun hada da jam'iyyar ADC, David Mark, Aregbesola, hukumar zabe mai zaman kanta da Ralph Nwosu.

Sauya alkalin ya zo ne makonni kadan bayan Kotun Koli ta umarci bangarorin da su koma Babbar Kotun Tarayya.

Nafiu Bala na kalubalantar bangaren David Mark a ADC
Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala Gombe da hoton jami'iyyar. Hoto: Hon. Nafiu Bala.
Source: Twitter

Bukatar kotun game da rikicin shugabancin ADC

Kotun Kolin ta bukaci a gaggauta sauraron karar domin kawo karshen rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Aisha Yesufu ta janye daga neman takarar sanata a jam'iyyar NDC

A ranar 30 ga Afrilun 2026, Kotun Koli ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya bukaci bangarorin su ci gaba da zama yadda suke.

Wannan umarni ne Hukumar Zabe ta Kasa ta yi amfani da shi wajen janye amincewa da shugabancin David Mark a baya.

Lokacin da aka sake sauraron karar a ranar 8 ga Mayu 2026, lauyan Bala, Luka Haruna, ya sanar da kotu sabon bukata.

Ya ce an aika wa Babban Alkalin Kotun Tarayya wasika domin neman a mayar da karar zuwa wani alkali daban, cewar Daily Post.

Nafiu Bala ya ƙaryata zancen yi masa barazana

Kin ji cewa shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafi’u Bala ya yi magana game da barazanar da aka ce an yi masa kan jam'iyyar adawa.

Nafiu Bala ya musanta rahoton da ke cewa ya yi nadamar rikicin jam’iyya tare da zargin rayuwarsa na cikin haɗari.

Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da farfaganda, yana mai cewa bai ba da wata hira ba kuma bai tura kowa ya yi magana madadinsa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.