Peter Obi ko Kwankwaso: NDC Ta Shirya Tsaida 'Dan Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

Peter Obi ko Kwankwaso: NDC Ta Shirya Tsaida 'Dan Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

  • Jam’iyyar NDC za ta gudanar da babban taro na musamman a Abuja domin tabbatar da Peter Obi a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027
  • Peter Obi ya zama ɗan takara taya tilo da ya nuna sha'awa sakamakon babu wani da ya sayi fom ɗin neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC
  • Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa an tantance Obi tare da amincewa da cancantarsa kafin taron tabbatar da shi a birnin tarayya na Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar adawa ta NDC ta sanar da cewa za ta gudanar da babban taro na musamman a ranar Asabar, 30 ga watan Mayu, domin tsaida dan takarar shugaban kasa.

NDC ta ce taron zai tabbatar da tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar LP a zaben 2023, Peter Obi, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya girma, ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027

Obi da Kwankwaso.
Peter Obi, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Seriake Dickson Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an shirya gudanar da taron ne a babban birnin tarayya Abuja yau Asabar.

Ana sa ran shugabannin jam’iyya NDC daga kowane mataki, wakilai daga jihohi daban-daban da magoya baya za su hallara domin nuna goyon baya ga takarar Obi.

NDC ta shirya tabbatar da Peter Obi

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar NDC, Osa Director, ya tabbatar da wannan lamari a wata tattaunawa da jaridar The Nation a Abuja.

A cewarsa, jam’iyyar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da taron cikin lumana da tsari.

Ya bayyana cewa taron zai kasance wata muhimmiyar alama a tafiyar siyasar jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Yadda Peter Obi ya zama ɗan takarar NDC

Rahotanni sun nuna cewa Peter Obi ne kaɗai ya sayi fom ɗin nuna sha’awa da kuma neman takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar NDC.

Saboda haka, babu wani ɗan takara da zai fafata da shi a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, lamarin da ya sa ya zama ɗan takara guda ɗaya da ke neman tikitin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Duk da rikicin PDP, tsagin Turaki ya ba Jonathan tikitin takarar shugaban kasa

Wannan ya bai wa jam’iyyar damar shirya taron musamman domin tabbatar da shi kai tsaye a matsayin wanda zai jagoranci tutar NDC a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

NDC .
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wurin taron NDC a Abuja Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kwamitin tantancewa ya amince da Obi

Kafin wannan mataki, kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC karkashin jagorancin Sanata Sam Egwu ya gayyaci Peter Obi domin tantancewa.

Bayan gudanar da aikin tantancewar, kwamitin ya bayyana cewa Obi ya cika dukkan sharuddan da jam’iyyar ta gindaya ga masu neman tikitin shugaban ƙasa.

Obi ya yi maganar takarar Jonathan

A wanu rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya tabo batun takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a zaben 2027.

Peter Obi ya yi watsi da rade-radin cewa Goodluck Jonathan, na iya zama barazana ga burinsa na takarar shugaban kasa a 2027.

Ya ce dimokuradiyya tana bai wa mutane damar neman mukami domin yi wa kasa hidima, sannan jama’a su zabe su bisa cancanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262