An Samu Barkewar Cuta a Borno, fiye da Mutane 25 Sun Mutu a cikin Watan nan

An Samu Barkewar Cuta a Borno, fiye da Mutane 25 Sun Mutu a cikin Watan nan

  • Rahoton lafiya ya nuna cewa mutum 2,715 ake zargin sun kamu da cutar kwalara a jihar Borno cikin kwanaki 24 na watan Mayun 2026
  • Akalla mutum 27 sun rasu yayin da birnin Maiduguri ya fi kowanne yanki fama da yawaitar masu dauke da cutar kwalara
  • Masana lafiya sun yi gargadi cewa adadin masu kamuwa da cutar na iya karuwa yayin bukukuwan Sallah idan ba a dauki matakin gaggawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - An sanu barkewar mummunar cutar kwalara a jihar Borno inda aka samu mutum 2,715 da ake zargin sun kamu da cutar.

Bayanan da aka samu sun kuma nuna cewa kimanin mutane 27 suka mutu sakamakon kawuwa da kwalara cikin kwanaki 24 na farkon watan Mayun 2026.

Cutar kwalara ta barke a Borno, mutane 27 sun mutu zuwa yanzu
Wani ma'aikaci yana feshin magani a dakin masu fama da cutar kwalara a Kano. Hoto: Michael Williamson/The Washington Post via Getty Images
Source: Getty Images

Cutar kwalara ta fara barna a Borno

Kara karanta wannan

Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki

Rahoton da Premium Times ta samu ya nuna cewa lamarin na kara ta’azzara cikin gaggawa yayin da ake samun karin masu dauke da cutar a cikin sa’o’i 24 kacal.

Jami’an lafiya sun bayyana cewa adadin mutane 2,715 da aka lissafo ba shi ne cikakken alkaluman ba saboda har yanzu ba a tattara bayanai daga wasu cibiyoyin kula da masu fama da kwalara da wuraren bayar da maganin ruwa ba.

Hakan ya kara jefa jama’a cikin fargaba musamman yayin da ake bukukuwan Sallah, lamarin da zai iya kara yada cutar cikin sauki.

Rahoton ya nuna cewa cutar ta bazu zuwa akalla unguwanni 29 da kuma al’ummomi 124 a sassa daban daban na jihar Borno.

Birnin Maiduguri ne ya fi fama da barkewar cutar inda aka samu mutum 1,568 da ake zargin sun kamu da ita.

Sauran kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Jere mai mutum 834, Mafa mai mutum 159, Konduga mai mutum 95 da Monguno mai mutum 56.

Haka kuma an samu mutum biyu da ake zargin sun kamu a Ngala yayin da aka samu mutum daya a Magumeri.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai mummunan hari Kwara, sun kashe masu ibada

Mutane 27 sun rasu sakamakon cutar

Daga cikin mutum 27 da suka mutu sakamakon barkewar cutar, mutum 11 sun rasu ne a cikin gari kafin kai su asibiti yayin da sauran mutum 16 suka mutu a cibiyoyin lafiya.

Rahoton ya nuna cewa kaso na mace-mace ya kai 1%, wanda ya yi daidai da matakin gaggawa na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

An kuma gano mutum 35 da suka nuna alamun kamuwa da cutar ta hanyar gwajin gaggawa yayin da mutum 14 aka tabbatar sun kamu da kwalara ta hanyar gwajin dakin gwaje-gwaje na kasa.

Fiye da mutane 25 sun mutu da cutar kwalara ta barke a Borno.
Taswirar jihar Borno, inda mutane 27 suka mutu bayan kamuwa da cutar kwalara.Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi bayani kan cutar kwalara

Kwalara cuta ce mai haddasa gudawa mai tsanani wadda ake kamuwa da ita ta hanyar cin abinci ko shan ruwa da ya gurɓace da kwayar cutar Vibrio cholerae.

Cutar na yaduwa cikin sauri musamman a wuraren da babu tsaftataccen ruwa, tsaftar muhalli mai kyau da kuma cunkoson jama’a, kamar yadda WHO ta wallafa a shafinta.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara yi wa mutane allurar hana kamuwa da cutar HIV a Najeriya

Hukumar WHO ta ce alamomin cutar sun hada da gudawa mai tsanani, amai da bushewar jiki, kuma idan ba a yi gaggawar magani ba tana iya kaiwa ga mutuwa cikin sa’o’i kadan.

Za a samu barkewar cututtuka a Arewa

A wani labari, mun ruwaito cewa, NCDC ta gargaɗi ƴan Najeriya game da bullar cutar gudawa da sauran cututtuka sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi hasashe a 2026.

Hukumar ta yi hasashen cewa za a samu bullar cututtukan a Kaduna, Kogi da jihohi takwas, wanda ya zama wajibi mazauna jihohin su dauki mataki.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu dai ya jaddada cewa gwamnatinsa na ba da fifiko ga magance ambaliya don tabbatar da wadatar abinci da tsaron rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com