Nazari: Ziyarar Tinubu a Jihar Katsina da Ra'ayin 'Yan Arewa gabanin Zaben 2027

Nazari: Ziyarar Tinubu a Jihar Katsina da Ra'ayin 'Yan Arewa gabanin Zaben 2027

Katsina - A makon da ya gabata ne shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wannan ziyara ta kwanaki biyu da shugaban kasar ya kai ita ce ta farko da Tinubu ya kai Katsina tun bayan hawansa mulki a watan Mayu, 2025.

Shugaba Tinubu.
Ana ganin zuwa Tinubu Katsina na da alaƙa da shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027 Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya ziyarci jihar Katsina

Kamar yadda fadar shugaban kasa ta wallafa a shafin X, Shugaba Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyukan da gwamnatin Katsina ta kammala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin ayyukan da Tinubu ya kaddamar har da Cibiyar Noma ta Zamani wadda gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya kafa domin bunƙasa harkokin gona.

To sai dai duk da fadar shugaban kasa ta ce ziyarar ta aiki ce amma ana ganin zuwa Tinubu mahaifar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wata dabara ce ta siyasa.

Masu sharhi kan harkokin siyasa da ƴan Arewa da dama na ganin zuwan Tinubu wata sabuwar dabara ce ta fara yaɗa manufarsa ta tazarce yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi nazari kan ziyarar Tinubu a Katsina da kuma ra'ayoyi da mahangar ƴan Arewa gabanin zaɓe na gaba.

Batun matsalar tsaro a Arewa

A yayin wannan ziyara, Shugaba Tinubu ya gana da dakarun sojojin Operation Fansan Yamma da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Katsina da jihohin Arewa maso yamma.

Da yake jawabi ga dakarun, Tinubu ya bayyana kudirin gwamnatinsa na inganta walwala da jin dadinsu da ƙara samar masu da kayan aiki.

Bola Tinubu.
Yadda Bola Tinubu ya gana da sojoji a lokacin da ya kai ziyara Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Ya sanar da shirye-shiryen kara albashi, samar da gidaje masu inganci, inshorar lafiya da tallafi ga iyalan dakarun sojin domin karfafa masu guiwa a yakin da suke da ƴan ta'adda.

Bugu da kari, an ware Naira biliyan 200 a kasafin kudin 2025 don gina sababbin barikin sojoji a Najeriya duk a ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na dawo da zaman lafiya.

Tinubu ya kaddamar da ayyukan raya ƙasa

Bayan nan Tinubu ya kaddamar da Cibiyar Inganta Noma ta Katsina, aikin da ya kai kimanin Naira biliyan 15, wanda zai taimaka wajen bunkasa noman zamani.

Sannan shugaban ƙasar ya bude hanyar mota mai tsawon kilomita 24 da Gwamna Dikko Raɗɗa ya gina a Katsina domin saukaka harkar sufuri da kasuwanci a yankin.

Wannan ayyuka sun kayatar da mai girma shugaban ƙasa, inda aka ji yana yabon Malam Dikko Raɗɗa da cewa shi mutum ne mai gaskiya da rikon amana, rahoton Premium Times.

Tinubu da Dikko.
Shugaba Tinubu ya yaba da salok mulkik gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Haɗuwa da ƴan siyasa da sarakuna

Bola Tinubu ya halarci bikin auren ɗiyar Gwamna Dikko Radda a gidan gwamnatin Katsina kuma ya halarci liyafar da aka shirya domin yi wa ma'auratan addu'o'i.

Shugaban ƙasar ya haɗu da manyan sarakuna, jiga-jigan siyasa da sauran shugabannin al'umma a wannan ziyara.

Gwamnoni daga jihohi daban-daban, tsofaffin gwamnoni, ƴan Majalisar jiha da na tarayya da ƴan kasuwa sun halarci bikin da aka yi ranar Asabar.

Wannan ya sa ake ganin ziyarar Tinubu a Katsina wata dabarar siyasa ce ta nuna irin abubuwan da gwamnatinsa ke yi domin inganta rayuwar jama’a, musamman a bangaren tsaro da ci gaban kasa.

Ra’ayoyin ƴan Arewa gabanin 2027

Ra’ayoyin ƴan Arewa game da ziyarar Shugaba Tinubu da yiwuwar sake goyon bayansa a zaɓen 2027 ya bambanta, wasu na ganin zai samu haɗin kansu kamar yadda suka yi a 2023.

Sai dai kuma akwai wasu da ke nuna damuwa da halin tsaro, matsin tattalin arziki da kuma rashin cika wasu alkawura da shugaban kasar ya ɗauka a lokacin kamfe, rahoton Tribune

Shugaba Tinubu.
Yan Arewa sun kafa sharadin sake zaben Bola Tinubu Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Twitter

Wani ɗan APC da ya je wurin tarbar shugaban kasa, Usman Bello ya shaidawa Legit Hausa cewa yadda Katsinawa suka fito tarbar Tinubu ya ba shi mamaki.

Ya ce dandazon mutanen da suka fito don tarbar shugaban kasa ya kara nuna cewa Arewa za ta sake ba shi dama karo na biyu a zaɓen 2027.

Usman ya ce:

"Jama'a sun fito fiye da tunaninka, duk da akwai waɗanda ƴan siyasa suka ɗauki nauyi amma akwai ƴan gari da suka fito bisa ra'ayin kansu.
"Wannan shaida ce da ke nuna Katsina sun gamsu da salon mulkin shugaban ƙasa kuma za su ƙara zaɓensa."

Amma ra'ayin wani malamin makaranta ya banbanta, inda ya shaidawa wakilinmu cewa akwai babban aiki a gaban Tinubu kafin ƴan Arewa su kara yarda da shi.

Malamin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce abu ɗaya da zai sa ya ƙara zaɓen Tinubu shi ne zaman lafiya ya samu a Katsina kuma tsadar kaya su sauka daidai talaka.

Idan har ya fito neman tazarce, Tinubu zai sa ran samun kuri'u daga Katsina kasancewarta mahaifar Muhammadu Buhari kuma jihar APC.

Tinubu ya ba gwamnoni mafita kan masu zagi

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnoni su daina daka ta masu sukar ayyukan da suke yi, su maida hankali wajen kyautatawa talaka.

Tinubu ya tabbatar wa gwamnonin cewa matukar suka yi wa jama'arsu abin da ya dace, ayyukan alherinsu kaɗai martani ga masu sukarsu.

Mai girma shugaban ƙasa ya ce burin irin waɗannan mutane kawai su ɗauke hankalin shugabanni daga sauke nauyun da ya rataya a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262