Bayan Batun Takarar Fubara, Kotu Ta Rusa Jagororin APC da ke wa Wike Biyayya
- Kotun daukaka kara da ke birnin Port Harcourt ta tabbatar da hukuncin babbar kotun jihar Rivers da ya soke tarukan jam’iyyar APC
- Taron ne ya samar da shugabannin kananan hukumomi da na jihar, wadanda suka samar da shugabannin da ke yi wa Nyesom Wike biyayya
- A ranar 20 ga Disamba, 2024, mai shari’a Godswill Obomanu na kotun Rivers ya bayar da umarnin wucin gadi da ya hana APC gudanar da taruka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Kotun daukaka kara da ke zama a Port Harcourt ta tabbatar da hukuncin babbar kotun jihar Rivers wanda ya soke tarukan APC da suka haifar da zaben Cif Tony Okocha da sauran mambobin kwamitin zartarwarsa a jihar.
Shugaban da aka kora da sauran mambobin kwamitinsa na daga cikin masu alaka da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Source: Facebook
Hukuncin da kotu ta yi a 2024
Daily Trust wallafa cewa mai shari’a Obomanu na babbar kotun jihar Rivers ya soke tarukan da APC ta gudanar a jihar Rivers a ranar 20 ga Disamba, 2024, wadanda suka haifar da fitowar Tony Okocha da sauran shugabannin jam’iyyar.
Bayan haka, shugabannin da aka kora sun shigar da kara a kotun daukaka kara domin neman a soke hukuncin mai shari’a Obomanu.
Hukuncin kotun daukaka kara
Da ta ke yanke hukunci a ranar Juma’a a Port Harcourt, mai shari’a Elfreida Oluwayemisi Williams-Dawodu ta kotun daukaka kara a Port Harcourt ta tabbatar da hukuncin babbar kotun jihar Rivers da ya soke tarukan.
A yanzu, duk wasu matakai da wakilcin da kwamitin zartarwa karkashin jagorancin Tony Okocha ya yi a madadin APC tun daga ranar 20 ga Disamba, 2024 zuwa yanzu sun zama marasa inganci, marasa tasiri.
Haka kuma, ’yan takarar da jam’iyyar ta tsayar gabanin babban zabe a jihar na iya fuskantar barazanar rashin cancanta.
Martanin APC a jihar Rivers
Da yake mayar da martani ga hukuncin, kwamitin zartarwa na APC karkashin jagorancin Tony Okocha ya ce babu wata barazana ga matsayinsa har sai an kammala shari’ar.
Sakataren Yada Labarai na APC a jihar, Chibike Ikenga ya ce kotun ta yanke hukunci ne kawai kan daukaka kara ta wucin gadi kuma ta mayar da batun zuwa kotun farko domin cikakken sauraron shari’ar.
Channels TV ta rahoto ya ce:
“Babu wata barazana ga matsayin kwamitin zartarwa har sai an kammala sauraron shari’ar. Lauyoyinmu za su yi nazarin cikakken hukuncin sannan su ba da shawara kan mataki na gaba."

Source: Facebook
Wike ya magantu kan Fubara
A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya sanar da cewa gwamna Siminalayi Fubara ya san ba zai nemi tazarce ba.
Wike ya ce tun a lokacin da aka yi wani zaman sulhu aka yi da shi cewa ba zai nemi takara a karo na biyu bayan ya gama wa'adinsa a 2027.
Martanin Nyesom Wike ya zo ne bayan gwamna Siminalayi Fubara ya ce ya fasa neman takara a karkashin APC a zaben 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng

