"A Maido Mini da Kudi na," Matar da Ta Fito Takarar Shugaban Kasa Ta Tada Rigima a DLA
- Abisayo Busari-Akinnadeju ta fice daga jam'iyyar DLA bayan gaza samun tikitin takarar shugaban kasa a babban zaben 227
- Matar ta ce ta yi haka ne bisa zargin shugabannin jam’iyyar da rashin gudanar da sahihin zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa
- Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da fafutuka domin tabbatar da ta shiga zaben shugaban kasa a 2027 kamar yadda ta kudirta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Matar da ta fito neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar DLA a zaben 2027, Misis Abisayo Busari-Akinnadeju, ta sanar da ficewarta daga jam’iyya.
Bayan ta fita daga DLA, matar da kuma nemi a maido mata da kudin fam din takarar shugaban kasa da ta siya saboda abin da ta kira rashin adalci a zaben fitar da gwani.

Source: Twitter
Punch ta ruwaito cewa Abisayo Busari ta bayyana hakan ne cikin wata wasika da ta aikewa shugaban jam’iyyar DLA na kasa, wacce aka samu a Akure ranar Juma’a.
Dalilin ficewar Abisayo daga DLA
A cikin wasikar, ‘yar siyasar ta bayyana cewa ta yanke shawarar barin jam’iyyar ne saboda abin da ta kira rashin gudanar da zaben fidda gwani cikin gaskiya da adalci.
Ta ce abin takaici ne yadda shugabannin jam’iyyar DLA suka yanke shawarar tsayar da dan takara ta hanyar maslaha maimakon bai wa ‘yan takara damar fafatawa cikin gaskiya.
A cewarta:
“Na rubuta wannan wasika ne domin sanar da kai da kuma kwamitin gudanarwa na kasa cewa na yi murabus daga jam’iyyar DLA nan take.
“Ban yi murabus saboda na gaza ba. Na yi murabus ne saboda ba a ba ni damar yin takara cikin gaskiya ba, kuma ba zan amince a hada sunana da tsarin da ya saba wa doka ba.”
Ta bukaci a mayar mata da kudin fam
Abisayo Busari ta kuma bukaci jam’iyyar da ta mayar mata da kudin fam din shugaban kasa da ta biya, tana mai cewa DLA ta kasa cika alkawarin gudanar da sahihin zaben fidda gwani.
Ta ce:
“Ina bukatar a tabbatar mini da an karbi wannan murabus dina a rubuce. Haka kuma ina neman a dawo mini da kudin fam na shugaban kasa da na biya, saboda jam’iyyar ba ta samar da adalci da tsarin da ta yi alkawari ba.
“Ina kuma neman a maido min da duk wasu takardu ko bayanai na kashin kai da suke hannun jam’iyyar ko jami’anta.”

Source: Facebook
Shin ta hakura da neman takara a 2027?
Duk da ficewarta daga jam’iyyar, Busari-Akinnadeju ta jaddada cewa har yanzu tana da burin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, kamar yadda Daily Nigerian ta kawo.
Ta ce manufofinta karkashin taken “Dare Nigeria” ba su canza ba, illa ma karfafa mata gwiwa da abin da ta gani a cikin jam’iyyar.
Ta kara da cewa za ta ci gaba da fafutukar ta ne a karkashin wata dandalin siyasa da ta ce ya dace da muradunta da kuma bukatun ‘yan Najeriya.
Atiku ya karbi tutar ADC gabanin zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa ysohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya karbi tutar ADC bayan lashe zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a 2027.
Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ne ya miƙa wa Atiku tutar a gaban shugabannin jam’iyya da dandazon magoya baya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya buƙaci sauran masu neman tikitin jam’iyya, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen, da su haɗa kai domin ci gaban ADC.
Asali: Legit.ng


