Tashin Hankali Yayin da Fusatattun Matasa Suka Kona Gidan Babban Basarake, An Yi Karin Bayani

Tashin Hankali Yayin da Fusatattun Matasa Suka Kona Gidan Babban Basarake, An Yi Karin Bayani

  • Wasu fusatattun matasa sun kona fadar babban basaraken jihar Edo, Olojah na Ojah, Oba Okogbe Lawani
  • Lamarin ya haifar da hatsaniya da tashin hankali a tsakanin mazauna garin Ojah da ke karamar hukumar Akoko-Edo
  • Rikicin ya samo asali ne a yayin binne wata mata da ake zargin ta mutu a cikin gidan tsafi a yankin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Oja, jihar Edo - An samu tashin hankali a garin Ojah da ke karamar hukumar Akoko-Edo ta jihar Edo.

Hakan ya kasance ne yayin da wasu matasa a garin suka kai farmaki tare da cinnawa fadar Olojah na Ojah, Oba Okogbe Lawani wuta, Nigerian Tribune ta rahoto a ranar Talata, 30 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka shugabannin matasa 2 a jihar PDP

Matasa sun kona fadar sarki a Edo
Tashin Hankali Yayin da Fusatattun Matasa Suka Kona Gidan Babban Basarake, An Yi Karin Bayani Hoto: Pious Utomi Ekpei, Emmanuel Arewa
Asali: Getty Images

Edo: Matasa sun kona fadar basarake

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa rigimar ta fara ne lokacin da wata mata ta mutu, kuma bayan bincike, sai aka gano cewa gidan tsafin Ojah ne ya kashe matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin kauyen ya ce:

"Wato al'ummar gari sun so su binne matar kamar yadda suka saba, wanda shine binne mutum a sama bi ma'ana jefa gawarwakin da ke gidan tsafin kan tsaunuka."

An rahoto cewa Oba Lawani ya hana irin wannan binnewar da ake yi wa gawa, amma sai matasan suka yi zargin rashin gaskiya tattare da basaraken wanda suke ganin ya gayyaci jami'an tsaro.

Wata majiya ta ce:

"A kan haka ne, matasan suka yanke shawarar fafatawa da jami'an tsaron, suka farmaki jami'an tsaron da duwatsu sannan suka kore su.
"Kuma a cikin fushinsu ne, sai suka farmaki fadar basaraken gargajiyan."

Kara karanta wannan

Yadda ma'aikacin banki ya yi karyar 'yan bindiga sun sace shi saboda bashin naira miliyan 1.7

Koda dai lamarin ya afku ne kwanaki biyu da suka gabata, jaridar Legit ta fahimci cewa har yanzu ana zaman dar-dar a yankin.

Da aka tuntube shi, kakakin 'yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ya ce har yanzu yana jiran rahotanni daga DPO na yankin, rahoton Independent.

Shehu Sani ya magantu kan kisan sarakuna

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi martani a kan kisan sarakuna biyu da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Ekiti.

A martaninsa a ranar Talata, 30 ga watan Janairu, Sani ya ce dole a hukunta wadanda suka hallaka sarakunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel