Yaran Turji na Cin Karensu ba Babbaka, Sun Kora Mazauna Sokoto, Zamfara daga Gidajensu

Yaran Turji na Cin Karensu ba Babbaka, Sun Kora Mazauna Sokoto, Zamfara daga Gidajensu

  • Bello Turji ya bai wa mazauna kauyuka wa’adin ficewa daga garuruwansu ko kuma su fuskanci hari kafin 4: 00 na yammacin ranar Lahadi
  • Barazanar da sauren hare-haren da Turji da yaransa ke kai wa mazauna kauyukan Zamfara da Sakkwato ya jefa jama'a a mawuyacin hali
  • Mazauna Bafarawa da wasu kauyuka sun tsere sakamakon barazanar da ‘yan bindiga ke yi, lamarin da ke kara tayar da hankali a Sokoto da kewaye

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Barazanar da fitaccen shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya yi sun tayar da wasu al’ummomi a Arewa maso Yammacin Najeriya daga muhallansu.

Rahotanni sun bayyana cewa an jefa mazauna jihohin Sakkwato Wannan na zuwa ne yayin da hare-haren kisa da satar mutane ke ci gaba da addabar jihar Zamfara.

Tsaro
DakarunBello Turji sun addabi mazauna Arewa maso Yamma Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Leadership News ya bayyana cewa al’ummar garin Bafarawa da ke karamar hukumar Isa sun tsere daga gidajensu bayan sababbin barazanar da Turji ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kauyukan da dakarun Bello Turji ke kai hari

Punch News ta ruwaito cewa Turji ya bai wa wasu kauyuka da suka hada da Kamara, Arume, da Kagara wa’adin barin garuruwansu kafin karfe 4 na yamma ranar Lahadi ko su fuskanci mummunan hari.

Karamar hukumar Isa na daga cikin wuraren da suka fi shan wahala daga hare-haren ‘yan bindiga a Sokoto.

Yaran Turji sun mamaye wasu kauyuka

Baya ga Bafarawa, sauran kauyukan da suka fuskanci irin wannan barazana sun hada da Surudubu, Gebe, Tsullawa, da Garin Fadama.

Da aka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufai, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun shiga yankunan da abin ya shafa.

Zagazola
Mazauna Sakkwato da Zamfara sun fara barin muhallansu saboda yaran Turji Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Ya ce:

“Duk da cewa ba mu samu korafi kai tsaye ba dangane da wannan barazana, jami’an mu suna can a cikin yankunan tun kwanaki uku da suka gabata kuma suna cikin shirin dakile duk wani barazana ga zaman lafiya da tsaro.”

A wani labarin makamancin wannan, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kisan wani tsohon malamin makarantar sakandare da kuma sace matarsa tare da wasu mata biyu.

Mummunan lamarin ya afku bayan ‘yan bindiga sun kai wa hari yankin Tsafe, da ke jihar Zamfara, lamarin da ya jefa jama'a a cikin mawuyacin hali na fargaba da firgici.

Makusancin Turji ya matsawa Sakkwatawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa an gano yadda babban hadimin Bello Turji na daga cikin wadanda ake zargi da kai wasu munanan hare-hare a kauyukan jihar Sakkwato.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa yaran Turji sun kai farmaki a wasu kauyuka da ke yankin gabashin Sakkwato, duk da cewa Turji da kansa yana neman mafaka daga sojojin kasar nan.

Hare-haren da aka kai sun jefa mazauna cikin fargaba, inda da dama daga cikinsu suka tsere daga gidajensu, suna neman mafaka a garuruwa mafi nisa domin guje wa farmakin yan bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.