"Kai Ma Yaro na ne," Ganduje Ya Dauko Tarihi yayin Maida Martani ga Kalaman Kwankwaso

"Kai Ma Yaro na ne," Ganduje Ya Dauko Tarihi yayin Maida Martani ga Kalaman Kwankwaso

  • Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya tuna yadda ya taimaka wa madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Kwankwaso tun farko
  • Ya dauko wannan tarihi ne a matsayin martani ga kalaman Kwankwaso, wanda ya kira Ganduje da yaronsa na siyasa
  • Ganduje ya ce bai kamata a tsaya tantance waye ubangidan wani ba, yana mai cewa uba na iya rainon dansa kuma daga baya ya fi shi daukaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya maida martani ga kalaman tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya yi ikirarin cewa a farkon siyasarsu, Kwankwaso "yaro na ne," inda ya ce ya taimaka wa madugun Kwankwasiyyar har ya tafi Majalisar dokoki ta kasa.

Kwankwaso da Ganduje.
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

Daily Trust ta ce Ganduje, wanda ke kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatansa, Muhammad Garba, ya fitar ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

"Ko Ganduje ba zai ce shi ba yarona ba ne": Kwankwaso ya yi martani ga Abba

Martanin ya biyo bayan wasu kalamai da aka alakanta da Kwankwaso, inda ya ce: “Ko Ganduje ma ya taba zama yaro na.”

Ganduje ya tuna yadda ya taimaki Kwankwaso

A cikin sanarwar, Ganduje ya ce siyasa tana ginuwa ne a kan dangantaka, goyon baya, jajircewa da kuma jagoranci, yana mai cewa babu wani dan siyasa da zai kai matsayi ba tare da taimakon wasu ba.

Ya ce tun a farkon siyasarsa, ya taimaki Kwankwaso musamman a lokacin zaben majalisar dokoki ta kasa da ya kai shi matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai.

“Lokacin nan Ganduje na da damar cewa Kwankwaso yaronsa ne, domin ya taimaka masa ta bangaren kudi da kuma goyon bayan siyasa,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta tuna lokacin Ganduje ya rike kujerar babban jami’in gwamnati a Abuja da kuma kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na Kano, lokacin da Kwankwaso ke yawan ziyartar ofisoshinsa domin neman shawara da hadin kai.

Ya bukaci a daina siyasar ubangida

Tsohon shugaban APC ya ce bai kamata siyasa ta koma batun “waye ubangidan wani,” ba, musamman a lokacin da jama’a ke sa ran shugabanni za su fi mayar da hankali kan ci gaba da walwalar al’umma.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso hatsari ne': Tsohon dan majalisar Amurka kan takarar jagora da Obi

Ganduje ya kuma tuna da zaben fidda gwani na gwamna a Kano a shekarar 1998, inda ya ce mutane da dama sun yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben.

A cewarsa, manyan ‘yan siyasa suka bukace shi da ya hakura domin hadin kai, ya amince ya zama mataimakin gwamna tare da Kwankwaso, kamar yada Daily Post ta kawo.

Ganduje.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Duk da sabanin siyasa da ya shiga tsakaninsu daga baya, Ganduje ya ce sun yi aiki tare cikin nasara daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan suka sake hada kai daga 2011 zuwa 2015 a matsayin gwamna da mataimaki.

“Ba daidai ba ne siyasa ta zama batun wanda ya fi wani. Uba na iya rainon da wanda daga baya ya fi shi daukaka da tasiri,” in ji Ganduje.

Kwankwaso ya tsaida dan takarar gwamna

A baya, an ji cewa magudun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da manyan wadanda za su yi wa NDC takara a Kano.

Kwankwaso ya ayyana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa NDC takarar gwamna a zaben 2027.

Kwankwaso ya kuma tabbatar da cewa Nasiru Yusuf Gawuna zai nemi Sanata a Kano yayin da Peter Obi zai yi wa NDC takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262