"Dogaran Sarki Sun Yi Ɓarna": Yadda Aka Yi Rikici a Wurin Bikin Auren Ɗiyar Gwamna Dikko

"Dogaran Sarki Sun Yi Ɓarna": Yadda Aka Yi Rikici a Wurin Bikin Auren Ɗiyar Gwamna Dikko

  • Wasu dogarai sun fasa gilashin ƙofa a lokacin da Mai Martaba Sarkin Katsina ya isa wurin bikin ɗiyar Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa
  • An ruwaito cewa dogaran Abdulmumin Kabir sun fusata har suka yi wannan ɓarna saboda jinkirin da aka samu kafin buɗewa sarki ƙofa
  • Bikin dai ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar Katsina ciki har da shugaban kasa watau Bola Ahmed Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Wani karamin rikici ya faru a lokacin da mai martaba sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman da tawagarsa suka isa wurin bikin auren ɗiyar Gwamna Dikko Raɗɗa.

An ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ƙofar shiga ɗakin taron da ke gidan gwamnatin Katsina ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, 2025.

Daura auren diyar Dikko Radda.
Dogaran sarki sun kawo cikas a wurin ɗaura auren diyar Gwamna Dikko Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ɗaurin auren ya samu halartar jiga-jigan siyasa a faɗin ƙasar nan ciki har da mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogaran Sarkin Katsina sun fasa ƙofa

Rahotanni sun bayyana cewa lokacin da sarkin ya karaso, an ɗan samu jinkiri kafin a ba shi dama ya shiga wurin.

Hakan ya sa dogaran sarkin suka fusata har suka fasa gilashin ƙofa saboda jinkirin da aka samu wajen ba mai martaba damar shiga ɗakin taron.

An shirya bikin ne a gaban manyan baƙi, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, tsofaffin gwamnoni da manyan ƴan siyasa a ciki da wajen Katsina.

Me yasa aka hana Sarkin Katsina shiga?

Sai dai an dakatar da shiga wurin na ɗan lokaci saboda tsauraran matakan tsaro na ofishin shugaban ƙasa.

Lamarin ya faru ne daidai lokacin da Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman, ya iso wajen, amma ya tarar da ƙofar a rufe.

A wani faifan bidiyo da Northern Blog ta wallafa a X, an ga dogaran sarki cikin kayan gargajiya suna ƙoƙarin bude ƙofar da karfi, wanda hakan ya sa suka fasa wani bangare na gilashin ƙofar.

Jami'an tsaro sun rufe ƙofar ne bayan Shugaba Tinubu ya shiga wurin, amma daga bisani dogarai suka fasa ƙofar mai martaba ya shiga.

Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman.
Yadda aka ɗan yi hargitsi a kofar shigs ɗakin taron bikin ɗiyar Gwamna Dikko Radda Hoto: Sheikh Abas
Asali: Facebook

Bidiyon abin da ya faru a wurin bikin

Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda baƙi suka firgita a lokacin da gilashi ya watse, sai dai jami’an tsaro da dogaran sarki sun shawo kan lamarin cikin gaggawa.

An bayyana cewa sarkin ya shiga cikin dakin taron ba tare da wata matsala ba, duk da haka an bar ƙofar da aka fasa a watse.

Daga bisani an ci gaba da harkokin bikin lami lafiya, inda Shugaba Tinubu, Gwamna Radda da sauran manyan baki suka yi addu'a da fatan alheri ga ma'auratan.

Za a rina: Yadda 'yan Arewa suka soki bikin

Tun kafin bikin ɗaurin auren ɗiyar Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa a jihar Katsina, wasu 'yan Arewa musamman a kafafen sada zumunta sun fara sukar bikin, suna danganta shi da nuna halin wuce gona da iri a lokacin da jama’a ke fama da matsin tattalin arziki.

Wasu na ganin an yi amfani da kudaden jama’a wajen gudanar da bikin da ya ja hankali, wanda hakan ya sa ake kallon bikin a matsayin nuna talakawa ba a bakin komai ba.

Wasu kuma sun bayyana damuwa da yadda aka sanya matakan tsaro fiye da kima, har ya hana wasu manyan baki shiga cikin sauki.

Sai dai duk da sukar da ake yi, bikin ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Katsina, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna cewa gwamnatin tarayya tana tare da jihar Katsina da Gwamna Raɗɗa.

Zuwa da halartar Shugaba Tinubu sun sauya yanayin zancen bikin a kafafen sada zumunta, inda wasu suka fara kallon bikin a matsayin taron siyasa da sada zumunci, ba wai na bikin aure kawai ba.

Rarara ya ƙayatar da Tinubu a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen mawakin nan, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya saki sabuwar waƙa a liyafar da aka shiryawa Bola Tinubu a Katsina.

Rarara ya cashe a gaban shugaban ƙasa da manyan bakin da suka ziyarci jihar Katsina wanda suka haɗa da gwamnoni, ƴan majalisa da sauransu.

Wakar dai ta ƙayatar da Shugaba Bola Tinubu wanda aka ga yana murmushi har da tafi a wurin liyarfar a daren ranar Juma'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262