Ana Wata ga Wata: Majalisar Wakilai na Shirin Kaɗa Ƙuri'ar Tsige Shugaban Ƙasa, Trump
- Wani 'dan majalisar Democrat ya gabatar da ƙudirin tsige shugaban Amurka, Donald Trump, kan zarge-zargen da suka hada da rashawa
- Jam'iyyar Republican na iya soke ƙudirin, yayin da shugabannin majalisar wakilan za su tattuna kan batun a cikin kwanaki biyu
- Fadar White House ta kira kudurin da "na rashin hankali" yayin da ta ce Trump bai aikata laifi ba, illa ma yana cika alkawuran da ya dauka ne
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Wani ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrat yana ƙoƙarin tilasta kaɗa ƙuri'a a majalisar kan ƙudurinsa na tsige Shugaba Donald Trump.
Ɗan majalisar wakilai, Shri Thanedar, D-Mich., ya gabatar da ƙudirin tsige Trump a matsayin mai fifiko a ranar Talata, wanda ke nufin majalisar na da kwanaki biyu kacal don tattauna kudirin.

Asali: Getty Images
An gabatar da kudurin tsige Trump a Amurka
Jam'iyyar Republican na iya yin ƙoƙarin soke ƙudirin ba tare da 'yan majalisar sun kaɗa ƙuri'a a kan batun a zauren majalisar ba, inji rahoton The Hill.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma ana ganin cewa ƙuri'ar tsige Trump da Shri Thanedar ya gabatar na iya jefa 'yan majalisar Democrat, marasa rinjaye a cikin mawuyacin hali.
An ce sai da jam'iyyar Democrat ta yi da-kyar kafin ta iya hada kan 'yan majalisar tun bayan zaɓen 2024, kuma irin wannan kuduri na iya zama haɗari a siyasance ga mambobinsu yayin da suke ƙoƙarin dawo da rinjayen majalisar a 2026.
Duk da haka, ana tsammanin cewa babu wani ɗan jam'iyyar Republican da zai goyi bayan tsige Trump, wanda ke nufin kudurin Thanedar zai sha kasa.
Zarge-zargen da dan majalisar ke yi wa Trump
Yayin da ya ke gabatar da ƙudirin tsige shugaban kasar, Thanedar ya shaida wa majalisar cewa:
"Donald Trump yana gudanar da aikinsa ba bisa ƙa'ida ba, yana jawo kaskanci ga kujerar shugaban ƙasa da mutanen Amurka.
Thanedar ya kuma yi ƙoƙarin sukar Ma'aikatar Inganta Gwamnati (DOGE) wadda Elon Musk ke jagoranta, yana mai kiran ta "ma'aikatar da aka ƙirƙira bisa saɓa wa kundin tsarin mulki."
Ɗan jam'iyyar Democrat ɗin, wanda ɗan asalin Indiya ne, amma yana wakiltar Michigan ya fara gabatar da makaloli bakwai na tsige Trump a ƙarshen Afrilu.
Sun haɗa da tuhume-tuhume na tauye adalci, zalunci, cin hanci da rashawa, da cin zarafin ikon kasuwanci da sauransu.

Asali: Twitter
Fadar White House ta yi martani
Lokacin da aka tuntube ta don yin tsokaci kan matakin dan majalisar, mai magana da yawun fadar White House, Liz Huston, ta shaida wa Fox News Digital cewa:
"Duk wani mataki da Shugaba Trump da gwamnatinsa suka ɗauka ya cika doka kuma ya samo asali ne daga son jama'ar Amurka.
"Shugaba Trump yana zartar da komai ne bisa alkawuran da ya dauka na: Tabbatar da iyakoki, jawo masu zuba jarin tiriliyoyin daloli a Amurka, da kuma dawo da shugabanci na-gari.
"A halin yanzu, 'yan Democrat suna sake nuna manufofinsu a fili, na; goyon bayan ci gaba da zaman baƙi ba bisa ƙa'ida, alhalin hakan na tauye jin daɗin 'yan ƙasar Amurka.
"Wannan ƙoƙari na tsige shi, na rashin hankali, ba komai ba ne illa wani matakin siyasa mai cike da rashin lissafi wanda jama'ar Amurka suka gani."
Albashin da ake biyan shugaban Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasar Amurka yana karɓar albashi na $400,000 a kowace shekara, wanda ake ɗauka daga kuɗin harajin da 'yan ƙasa ke biya.
A lokacin mulkinsa na farko, Shugaba Donald Trump bai karɓi albashi ba, sai dai ya raba kuɗin ga ma'aikatun gwamnati don tallafa wa ayyukan gwamnati.
Bayan sauka daga mulki, tsohon shugaban ƙasar Amurka zai ci gaba da karɓar $244,000 a kowace shekara, tare da samun tsaro, kula da lafiya, da tallafin tafiye-tafiye na gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng