'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sake Farmakar Sansanin Sojoji, An Yi Barna
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci kan sansanin sojojin Najeriya da ke jihar Borno a yankin Arewa maso Gabas
- Tsagerun ƴan ta'addan sun hallaka sojojin da ba a san adadinsu ba a harin da suka kai a cikin daren ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:00
- Ƴan ta'addan sun kuma kama wasu daga cikin sojojin da ke sansanin tare da ƙona tankokin yaƙi da kwashe makamai masu tarin yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ana zargin ƴan ta’addan Boko Haram da kai hari kan wani sansanin sojojin Najeriya da ke ƙaramar hukumar Marte a jihar Borno.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kashe sojoji waɗanda ba a bayyana adadinsu ba a yayin harin da suka kai.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majiyoyi daga cikin mutanen yankin da na tsaro sun tabbatar da aukuwar harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Boko Haram sun farmaki sojoji
Majiyoyin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a sansanin Forward Operation Base (FOB) na Bataliya ta 153 Task Force da kimanin ƙarfe 3:00 na daren ranar Litinin.
Ɗaya daga cikin majiyoyin, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya bayyana cewa an kori sojojin, aka kama da dama daga cikinsu a yayin harin.
Majiyar ta ƙara da cewa ƴan ta'addan sun ƙona tankokin yaƙi tare da kwashe makamai masu yawa daga sansanin.
“ISWAP sun karɓe Marte. An kashe wasu sojoji da ba a san adadinsu ba, an kama wasu, kuma da dama sun tsere. Sun nufi Dikwa, kuma yanzu suna a 24 Task Force Brigade, Dikwa."
"Ƴan ta’addan sun ƙona tankokin yaƙi sannan suka kwashe makamai da alburusai daga sansanin."
- Wata majiya

Asali: Original
Sojojin sama sun yi shawagi
Marte na da tazarar kilomita 38 daga Dikwa, hedikwatar ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Wata majiya daga Dikwa ta bayyyana cewa an ji harbe-harbe kuma jirgin yaƙin rundunar sojojin saman Najeriya ya yi shawagi a yankin.
Wannan harin dai na daga cikin jerin hare-haren da ƴan ta'addan Boko Haram suke kai wa a sansanonin dakarun sojojin Najeriya.
Karanta wasu labaran kan Boko Haram
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun ga ta kansu, babban hafsan sojojin kasa ya koma Borno
- Boko Haram ta sauya salo, ta koma amfani da 'jirage' wajen kai hare hare Borno
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun dasa bama bamai a Borno, an rasa rayukan sojoji
Ƴan Boko Haram sun hallaka babban soja a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun hallaka babban soja mai matsayin Kyaftin a harin da suka kai a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kashe Kyaftin ɗin ne tare da wani soja guda ɗaya a harin da suka kai a ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar.
Sarkin Gwoza, mai martaba Mohammed Shehu Timta, wanda ya tabbatar da aukuwar harin, ya bayyana cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin ƴam ta'addan a artabun da suka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng