Dalibai Sun Tallafa wa Tinubu da Miliyoyin Kudi domin Sayan Fom Din Takara
- Wasu daliban da suka ci gajiyar shirin NELFUND sun nuna farin cikinsu game da tallafi daga gwamnatin Bola Tinubu
- Daliban sun bayyana goyon baya ga shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027
- Sun kuma tara Naira miliyan 10.7 domin taimaka wa Tinubu wajen sayen fom din nuna sha’awar tsayawa takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Daliban da suka ci gajiyar Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND, a Anambra sun nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Daliban sun nuna goyon bayansu ne ga Tinubu domin ya sake neman mulki a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Twitter
Dalibai sun ba Tinubu gudummawar N10m
Shugaban kungiyar NANS JCC a Anambra, Ifeanyichukwu Chukwuemeka, ya ce sun yanke shawarar ne saboda sauye-sauyen ilimi da gwamnatin Tinubu ta kawo wa matasa, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Rikicin Yobe: mutum 6 da aka hana takarar gwamna a APC sun gana da Kashim Shettima
Ya ce matakin ya biyo bayan yadda shirin ya rage musu matsin kudin makaranta tare da kara samun damar shiga manyan makarantu.
Chukwuemeka ya ce daliban sun hada Naira miliyan 10,735,500 domin tallafawa sayen fom din nuna sha’awar takarar shugaban kasa ga Tinubu.
Ya bayyana cewa gudunmawar wata alama ce ta nuna godiya ga manufofin shugaban kasar wajen fadada damar samun ilimin gaba da sakandare.
Ya kara da cewa sun yaba wa gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, saboda irin goyon bayan da yake bai wa daliban jihar da kuma kokarinsa wajen inganta matsayin ilimi a fadin Anambra baki daya.

Source: Facebook
Musabbabin nuna goyon bayansu ga Tinubu
Daliban sun bayyana cewa nasarar wannan gangami ta samu ne sakamakon hadin kai da shawarwarin shugabanni da masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen bunkasa harkokin matasa da kungiyoyin dalibai a yankin Kudu maso Gabas.
Har ila yau, sun yabawa fitaccen dan kasuwa Obinna Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen karfafa gwiwar matasa da samar musu damar ci gaba, cewar Tribune.
Kungiyar ta kuma yabawa shugabar mata ta kungiyar City Boys Movement a Anambra, Adaora Soludo, da mai kula da kungiyar a jihar, Nonso Ozoemena, saboda kokarinsu wajen hada kan matasa da bunkasa shugabanci.
Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai tsohon mataimaki na musamman ga gwamna Soludo kan harkokin dalibai, Okoye Mathew, tare da shugabannin kungiyoyin dalibai daga cibiyoyin karatu daban-daban.
Matasa sun saya wa Pantami fom din takara
Mun ba ku labarin cewa magoya bayan Sheikh Isa Ali Pantami sun tara masa kudin fom din takarar gwamna a jihar Gombe karkahsin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Hakan na zuwa ne yayin da manufar tsohon ministan ta neman gwamna a jihar Gombe a zaben shekarar 2027 ke kara karfi bayan tsayar da dan takarar APC da tsohon ministan ya ki amincewa da haka.
Bayan tara miliyoyin kudi, matasan sun saya wa Pantami fom har an mayar da shi domin tabbatar da takararsa yayin da ya ke jiran zaben fitar da gwani kai tsaye.
Asali: Legit.ng
