Tinubu Ya Tura Ribadu Amurka, Ya Gana da Mataimakin Trump
- Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya tattauna batun yaki da ta'addanci tare da mataimakin shugaban Amurka
- Gwamnatocin Najeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri da kuma haɗin kan soja domin yaƙar Boko Haram da sauransu
- Shugaba kasa Bola Tinubu ya nuna godiya bisa ci gaba da tallafin horaswa da bayanan sirri da gwamnatin Amurka ke bai wa jami’an tsaron Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na Najeriya, Nuhu Ribadu, ya gudanar da wata ganawa ta manyan jami’an tsaro a Amurka.
Ganawar ta hada da mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance da ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio kan ƙoƙarin yaƙar ta’addanci a yammacin Afirka.

Kara karanta wannan
TUC ta kawowa Tinubu hanyar karya farashin fetur ta hanyar alaka da matatar Dangote

Source: Twitter
The Cable ta rahoto cewa tattaunawar su ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka yayin da ƙasashen biyu ke ƙara ƙaimi wajen yaƙar ƙungiyoyin ta’addanci.
Abubuwan da aka tattauna da Nuhu Ribadu
An bayyana cikakkun bayanan ganawar ne a cikin wata sanarwa da Secure Nigeria ta wallafa a shafinta na X, inda ta bayyana tattaunawar a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwa mai faɗi da ke da nufin tunkarar matsalar rashin tsaro.
A cewar sanarwar, tattaunawar ta sake tabbatar da haɗin kan da ke gudana tsakanin ƙasashen biyu wajen musayar bayanan sirri, horas da sojoji da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci.
“A wannan makon, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na Najeriya, Nuhu Ribadu, ya gana da Mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance da Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio, inda suka ƙarfafa haɗin gwiwar Amurka da Najeriya wajen tinkarar ta’addanci a yammacin Afirka,”
In ji sanarwar.

Source: Twitter
Tinubu ya yaba da tallafin Amurka
Sanarwar ta ce shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da nuna godiya bisa tallafin da gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Donald Trump ke bayarwa.
Ta ƙara da cewa tallafin Amurka wajen bayar da bayanan sirri da horas da jami’an soja na ci gaba da taimaka wa jami’an tsaron Najeriya a hare-haren da suke kai wa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Donald Trump bisa haɗin gwiwa da kuma ci gaba da tallafin horaswa da bayanan sirri daga Amurka yayin da jami’an tsaron Najeriya ke ƙara ƙaimi wajen rusa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda, kare Kiristocin Najeriya da kuma kare sauran al’ummomin da ke cikin haɗari,”
In ji sanarwar.
Amurka ta fitar da gargaɗin tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Donald Trump ta fitar da gargaɗin tafiye-tafiye zuwa Najeriya, inda ta gargadi ’yan ƙasar Amurka da su guji ziyartar wasu jihohi.
Gargaɗin kasar Amurka ya biyo bayan ƙarin damuwar tsaro, duk da cewa jami’an gwamnatin Najeriya sun ce suna matukar kokarinsu.
Amurka ta lissafa jihohin Plateau, Jigawa, Kwara, Neja Taraba cikin jerin wuraren da aka shawarci Amurkawa da kada su ziyarta saboda matsalar tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

