Majalisar Dattawa Ta Damu kan Hare Haren Boko Haram, Ta ba Sojoji Umarni

Majalisar Dattawa Ta Damu kan Hare Haren Boko Haram, Ta ba Sojoji Umarni

  • Majalisar dattawan Najeriya ta nuna damuwa kan yawaitar hare-haren ƴan ta'addan Boko Haram da kuma ISWAP
  • Babban mai tsawatarwa na majalisar ya gabatar da ƙudiri kan ƙaruwar sababbin hare-haren da ƴan ta'addan suke kai wa
  • Bayan sauraron ƙudirin, majalisar ta buƙaci a ƙara tura dakarun sojoji da kayan aiki zuwa jihohin Borno da Yobe domin shawo kan matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta buƙaci rundunar sojoji da ta sake tura dakarunta tare da kayan aiki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe.

Majalisar dattawan ta buƙaci hakan ne domin mayar da martani ga sababbin hare-haren da mayaƙan Boko Haram suke kai wa a jihohin.

Majalisar dattawa
Majalisar dattawa ta bukaci a tura sojoji zuwa Borno, Yobe Hoto: @NigerianSenate, @HQNigerianArmy
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta rahoto cewa majalisar dattawan ta cimma wannan matsayar ne yayin zamanta na ranar Talata, 13 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gabatar da ƙudiri kan hare-haren Boko Haram

Majalisar ta amince da hakan ne bayan gabatar da ƙudirin da babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Tahir Monguno, ya yi.

Sanata Monguno ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun kai harin kwanton ɓauna inda suka kashe fiye da dakarun sojoji masu yawa a garin Marte, wanda ke cikin ƙaramar hukumar Monguno.

Ya ƙara da cewa wani hari ya sake faruwa da safiyar Talata a Gajiram, hedikwatar ƙaramar hukumar Nganzai, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

"Majalisar Dattawa ta lura da cewa shekaru kadan da suka gabata, Boko Haram na da iko a fiye da kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomi a jihar Borno."
“Amma ta hanyar hadin gwiwar sojoji da ƴan sa kai, an kwato waɗannan yankuna, kuma an dawo da ƴanci da walwala ga mazauna wuraren."

- Sanata Mohammed Tahir Monguno

Ya ƙara da cewa yanzu ƴan ta’addan na amfani da fasahar zamani kamar jirage marasa matuƙa, da kuma nakiya, wanda hakan ke ƙara haddasa asarar rayuka ga sojoji da fararen hula, da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar mutane a yankin.

Sanata Abbas Aminu mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya ya mara wa ƙudirin baya, yana mai cewa ya kamata a haɗa da jihar Adamawa a cikin matakin da za a ɗauka.

Majalisar dattawa
Majalisar dattawa ta ce a tura sojoji zuwa Yobe da Borno Hoto: @Nigeriansenate
Asali: Facebook

Majalisa ta ce a tura ƙarin sojoji zuwa Borno, Yobe

Bayan tattaunawa, majalisar dattawa ta bukaci manyan hafsoshin sojoji da su sake tura isassun dakarun soja zuwa yankin Arewa maso Habas tare da basu kayan aiki na zamani domin tunkarar barazanar da ke ƙara ta’azzara.

Haka kuma majalisar ta umurci kwamitocinta kan harkokin sojoji da na rundunar sama da su sanya idanu wajen tabbatar da aiwatar da wannan ƙudiri.

Zulum ya yi alhinin hare-haren Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi Allah wadai da sababbin hare-haren ƴan ta'addan Boko Haram.

Gwamna Zulum ya yi alhini ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren na ƴan Boko Haram.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin magance matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng