Dan Majalisa Ya Fadi dalilin da Ya Sa Ya Zubar da Hawaye kan Rasa Tikitin Takara a Borno

Dan Majalisa Ya Fadi dalilin da Ya Sa Ya Zubar da Hawaye kan Rasa Tikitin Takara a Borno

  • Dan majalisar dokokin Borno mai wakiltar Magumeri, Audu Mustapha Ganga, ya yi magana kan rasa tikitin takara
  • Mustapha ya bayyana cewa hawaye da aka gani a bidiyo na farin ciki ne daga goyon bayan jama’a
  • Ya ce mutane sama da 100 daga mazabarsa ne suka hada kudi suka saya masa fom domin ya sake neman kujerarsa a zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan majalisar dokokin Borno mai wakiltar karamar hukumar Magumeri, Audu Mustapha Ganga, ya magantu kan takara.

Dan majalisar ya yi karin haske kan wani bidiyo da ya yadu yana zubar da hawaye a bainar jama’a.

Dan majalisar Borno ya fayyace dalilin zubar da hawaye
Dan majalisar Borno, Audu Mustapha yayin da yake zubar da hawaye a gaban magoya bayansa. Hoto: Mohammed Saleh Visuals.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Dr. Babakura Bukar, ya sanya wa hannu da Daily Trust da samu.

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Bidiyon da aka yada na ɗan majalisar Borno

Legit Hausa ta ruwaito yadda bidiyon dan majalisar ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masu bibiyar harkokin siyasa a kasar.

An ce dan majalisar bai yi kasa a gwiwa ba wajen neman ya sake zarcewa kan kujerarsa, cewar Aminiya.

Dan majalisar na jam'iyyar APC wanda ya kwashe shekaru a kan kujerar, ya roki masu ruwa da tsaki na mazabarsa da su sake ba shi dama.

'Dalilin zubar da hawaye na': Dan majalisa

A cewar sanarwar, hawayen da Mustapha ya zubar ba na bakin ciki ba ne, illa farin ciki saboda irin goyon bayan da jama’ar mazabarsa suka nuna masa.

Sanarwar ta bayyana cewa mutane sama da 100, musamman marasa karfi daga mazabarsa, sun hada kudi tare domin saya masa fom din takarar sake neman kujerarsa.

Mustapha ya bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin da ake yadawa inda ya ce bai kamata ba.

Kara karanta wannan

An soki Ganduje kan kalamai mabambanta game da sahihancin sarautar Sanusi II

An ce mutanen sun mika masa fom din ne tare da rokon ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027 domin ci gaba da wakiltarsu a majalisar dokoki.

Sanarwar ta ce sabanin rahotannin da ake yadawa, Mustapha bai yi kuka saboda neman a ba shi tikitin takara ko rokon sake zabe ba.

Dan majalisar Borno ya yi ƙarin haske kan zubar da hawaye
Audu Mustapha Ganga tare da fom din neman takara na APC Hoto: Grema Ali Wakilbe.
Source: Facebook

'Har yanzu APC bata cire dan takara ba'

Haka kuma, dan majalisar ya jaddada cewa babu wani dan takara da jam’iyyar APC ta tantance ko hana tikiti a wannan lokaci kafin gudanar da zabukan fitar da gwani.

Ya ce har yanzu APC ba ta kammala shirye-shiryen tantance ‘yan takarar mukaman zabe ba, saboda haka rade-radin da ake yadawa ba su da tushe.

Mustapha ya kuma bukaci jama’a su rika dogaro da sahihan bayanai daga majiyoyi masu inganci kawai, maimakon yada jita-jita daga kafafen sada zumunta.

Zulum ya nemi afuwar yan Borno

A baya, an ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya roki masu ruwa da tsakin APC da sauran al'ummar jihar Borno su masa afuwa idan ya bata masu.

Gwamna Zulum ya zubar da hawaye yayin da yake neman afuwa a taron APC da aka shirya domin jaddada goyon bayan tazarcen Tinubu/Shettima.

Mai girma Gwamna Zulum ya bukaci ‘yan jam’iyyar su hada kai domin tabbatar da nasarar APC a babban zaben 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.