Shugaba Tinubu Ya Aika Muhimmin Sako ga Masu Sukar Gwamnatinsa
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓo batun sukar da ake yi wa wasu daga cikin manufofin gwamnatinsa
- Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa yana maraba da yin suka mai ma'ana domin kawo gyara ga yadda yake tafiyar da mulkin ƙasar nan
- Sai dai, shugaban ƙasan ya nuna cewa sukar da ake yi masa ba za ta kawar masa da hankali ba wajen yin abin da ya dace ga Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan sukar da ake yi wa gwamnatinsa.
Tinubu ya ce zai ci gaba da maida hankali wajen yin abin da ya dace duk da sukar da ake yi wa manufofinsa.

Asali: Twitter
Sule Lamido ya ƙaddamar da littafi
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ƙaddamar da littafin mai suna 'Being True To Myself' a cibiyar taro ta NAF da ke babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban ƙasan ya samu wakilcin ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris a wajen taron, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Me Tinubu ya ce kan masu sukarsa?
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ƴan Najeriya na da ƴancin yin suka ga gwamnatinsa cikin gaskiya da adalci.
“Shugaban ƙasa yana maraba da duk wata suka mai ma’ana a kowane lokaci a ƙarƙashin ƴancin fadin albarkacin baki a tsarin dimokuradiyya, amma hakan ba zai sa a kawar masa da hankali daga yin abin da ya dace da Najeriya ba."
- Mohammed Idris
Tinubu ya taya Sule Lamido murna bisa ƙaddamar da littafin, yana mai bayyana shi a matsayin gagarumar gudunmawa ga adabin siyasa da tattaunawa kan dimokuradiyya a Najeriya.
“Wannan ba kawai ƙaddamar da wani littafi ba ne. Wannan biki ne na rayuwa mai cike da jarumtaka, daidaito da kishin gaskiya ga dimokuradiyya."
“Sule Lamido, ko da yake mamba ne na adawa kuma sau da yawa yana suka ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR), yana ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban siyasar Najeriya.”
- Mohammed Idris

Asali: Facebook
Tinubu ya yaba da littafin Sule Lamido
Shugaban ƙasan ya ce littafin yana bayyana Sule Lamido a matsayin ɗan siyasa, dattijo wanda ya tsaya tsayin daka da gaskiya.
Tinubu ya ce yana ba da shawarar karanta littafin ga dalibai, masana, ƴan jarida da ƴan siyasa, inda ya ce za su ci moriyar abin da ke cikin littafin na tsawon shekaru masu zuwa.
Uba Sani ya yabi Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yabi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Uba Sani ya haska wani ɓangare guda ɗaya wanda Mai girma.Bola Tinubu ya yi wa sauran shugabanni da suka jagoranci Najeriya fintinkau.
Uba Sani ya bayyana cewa a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da ta taɓa zuba jari a fannin noma kamar yadda gwamnatin Bola Tinubu ta yi a cikin shekara biyu kacal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng