TUC Ta Kawowa Tinubu Hanyar Karya Farashin Fetur ta hanyar Alaka da Matatar Dangote

TUC Ta Kawowa Tinubu Hanyar Karya Farashin Fetur ta hanyar Alaka da Matatar Dangote

  • Kungiyar kwadago ta TUC ta yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta dauki matakin saka tallafi a bangaren man fetur domin saukakawa talakawa
  • Hakan na zuwa ne yayin da yakin da ake a tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila ya jawo tsadar man fetur a Najeriya da wasu kasashen duniya
  • Tun bayan hawan shugaba Bola Tinubu mulki a 2023 ya cire tallafin man fetur kuma gwamnatin shi ta sha nanata cewa ba za ta dawo da shi ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta ba da shawarar sanya tallafi ga matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai domin taimakawa wajen rage farashin man fetur.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya fama da tsadar rayuwa, musamman bayan farashin man fetur ya tashi sosai a kwanan nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura Ribadu Amurka, ya gana da mataimakin Trump

Yadda ake sayar da mai a Najeriya
Mutane na sayen man fetur a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan ranar Juma’a yayin da yake amsa tambayoyi a shirin Politics Today a tashar Channels TV.

Kiran saka tallafin man fetur

Osifo ya ce tun da gwamnatin tarayya ta dage cewa ba za ta dawo da tallafin fetur ba, dole ne shugabannin ƙasar su nemo hanyoyin rage raɗaɗin tashin farashin mai.

“Mu a matsayin kasa Najeriya, muna samun kuɗi masu yawa. Fiye da abin da muka tsara a kasafin kuɗi. Yanzu haka muna samun aƙalla dala 35 ko fiye a kowace ganga sama da abin da muka tsara,”

In ji Osifo a shirin.

“Saboda haka abin da muka ba da shawara, ganin cewa ba sa son dawo da tallafin amfani, shi ne shugabanni su yi tunanin samar da wani irin tallafi. Tallafin da ake magana a kan shi ne, a yau muna da ƙananan matatun mai, ko ba haka ba?

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu

“Don haka muna cewa daga wannan ƙarin dala 35 da ake samu a kowace ganga, me zai hana a ɗauki rabinsa a yi amfani da shi wajen tallafa wa ɗanyen man da ake bai wa matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai, domin su samar da fetur mai rahusa?”
Yadda ake sayar da man fetur a Najeriya
Ana sakawa mota man fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda mai ya tashi a Najeriya

Tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran, farashin fetur ya tashi daga kusan N800 zuwa kusan N1,300 gwargwadon yankin da ake sayar da shi.

A kashin haka Osifo ya buƙaci gwamnati da ta:

“Yi tunanin wata sabuwar hanya tare da gaggauta ɗaukar matakan taimaka wa ’yan ƙasa.”

Wahalar da ake sha kan tsadar mai

A wata tattaunawa da wani dan kasuwa, Malam Muhammad Adamu, ya bayyana cewa tsadar mai yana shafar yadda suke jigilar kaya.

Ya ce:

"A yanzu, muna kashe kudi sosai wajen sayen man fetur. Yawanci kudin mu na tafiya wajen masu man fetur.
"Wani lokaci ma babu wata ribar da ake samu. Da za a dauki matakin rage kudin da an samu sauki sosai."

Babu batun maido tallafin fetur

A wani labarin, kun ji cewa duk da kiraye-kirayen da ake yi na dawo da tallafin fetur, gwamnatin tarayya ta dage cewa ba za ta sauya matsaya ba.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta sauya farashin fetur bayan yin karin N75 kan kowace lita

Ministan kudi, Taiwo Oyedele ya ce ba za a dawo da tallafin mai ba saboda yana kawo tangarɗa ga tattalin arziƙi, sannan ba za su sanya dokar daidaita farashi ba.

Ya bayyana cewa halin da ake ciki a Iran ya kawo wa Najeriya sababbin damammaki yayin da duniya ke neman hanyoyin samun makamashi daga wurare daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng