'Ba a Saba Gani ba': Ɗan Shekara 18 Ya Dirka wa 'Yan Mata 10 Ciki a Wata 5

'Ba a Saba Gani ba': Ɗan Shekara 18 Ya Dirka wa 'Yan Mata 10 Ciki a Wata 5

  • Kwararru sun tabbatar da cewa ɗan shekara 18 zai iya ɗirka wa mata 10 ciki cikin watanni biyar, amma sun ce ba a saba gani ba
  • A jihar Anambra ne aka rahoto cewa dan shekara 18 ya yi wa mata 10 ciki, kuma har da 'yar ubangidansa, a cikin wata biyar kacal
  • Yayin da masanan suka nemi a zurfafa bincike kan lamarin, Dakta Joseph Akinde ya ce akwai yiwuwar yaron na da cutar karfin sha'awa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Kwararru kan harkokin lafiyar jima'i sun tabbatar da cewa yana yiwuwa a ilimin halitta wani ɗan shekara 18 ya ɗirka wa mata 10 ciki a cikin watanni biyar.

Wannan ya biyo bayan wani lamari da ya faru kwanan nan a jihar Anambra da ya shafi wani ɗan shekara 18 da ke koyon aiki, da ake zargi da ɗirka wa mata 10 ciki, cikinsu har da 'yar maigidansa.

Masana ilimin jima'i sun ce ba a saba ganin dan shekara 18 ya dirka wa 'yan mata 10 ciki a wata 5 ba
'Yan mata 10 da ake zargin dan shekara 10 ya dirka wa ciki a wata 5 a jihar Anambra. Hoto: Anosike Stella.
Asali: Facebook

Yayin da masanan suka ce hakan na iya yiwuwa a ilimance, amma sun bayyana lamarin a matsayin abin da ba a saba gani ba, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masana sun magantu kan yi wa mata 10 ciki

Lamarin, wanda ma'aikatar mata da jin dadin jama'a ta jihar Anambra ke bincike a kai, ya jefa mutane a damuwa game da halayyar jima'i a tsakanin matasa da kuma yiwuwar cin zarafi.

Lamarin ya kuma bar mutane cikin tambayar kansu, yadda matashin ya iya shawo kan dukkanin 'yan matan, har suka yarda ya yi jima'i da su.

Likitocin mata, a tattaunawa daban-daban da jaridar, sun kuma bayyana cewa matashin na iya samun sha'awar jima'i mai yawa da kuma son yin jima'i da mata da yawa, wani yanayi da aka sani da 'nympomania'.

Kwararrun kan harkokin lafiyar jima'i sun kuma yi kira da a gudanar da bincike kan lamarin don tabbatar da cewa abin bai da alaƙa da hanyoyin samar da jarirai a yankin ba.

'Ba a saba gani ba' - Farfesa Chris Aimakhu

Da yake tsokaci kan lamarin, wani farfesa a fannin haihuwa da kuma cututtukan mata a jami'ar Ibadan, jihar Oyo, Chris Aimakhu, ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba a saba gani ba.

Afrfesa Chris ya ce:

"Akwai matsala, ace mata 10 da su yarda su kwanta da ɗan shekara 18, wanda ke koyon aiki, kuma ba shi da wani kudi da zai ba su."

Ya nuna damuwarsa cewa wataƙila wata ƙungiyar masu sayar da jarirai na amfani da matashin a wani tsari na haɗin gwiwa don samar da jarirai da nufin sayar da su.

Hakazalika, masanin ya yi kira ga hukumomi da su gudanar da gwajin DNA don tabbatar da cewa matashin ne ya yi wa dukkanin matan ciki.

Ya lura cewa:

"Ba dukkanin mata da suka kwanta da namiji ke ɗaukar ciki ba. Idan ya dirka wa 10 ciki, to wataƙila ya kwanta da mata 20. Dole dai a zurfafa bincike."

Ana zargin dan shekara 18 da ya dirka wa mata 10 ciki a Anambra na da matsalar karfin sha'awa
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Anambra. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ana fargabar yaron na da cutar karfin sha'awa

Shi ma da yake magana, ƙwararren likitan haihuwa da cututtukan mata, Dakta Joseph Akinde, ya tabbatar da cewa yanayin yana yiwuwa a likitance.

Sai dai yana ganin cewa yaron na iya fama da cutar karfin sha'awar jima'i, kuma mai son yin jima'i da mata daban daban, wanda a likitance ake kira 'Nympomania'.

Likitan matan ya bayyana nympomania a matsayin cutar ƙwaƙwalwa da karfin sha'awar jima'i, yana mai cewa ya kamata a kai matashin ya ga likitan ƙwaƙwalwa.

'Dan shekara 17 ya yi wa mata 10 ciki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Ribas ta bayyana cewa jami'anta sun yi nasarar kama wani dan shekara 17 da ya dirka wa mata 10 ciki a jihar.

An kama wanda ake zargin tare da wasu a wurare daban-daban da ke tsakanin ƙananan hukumomin Obia/Akpor da kuma Ikwerre, a inda ake sayar da jarirai.

'Yan sandan sun ceto mata 10 masu juna biyu, kuma sun gano cewa ana bai wa kowace mace N500,000 bayan ta haihu, sannan a sayar da jariran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.